Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu

Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu

- Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Ahmed Song, rasuwa ranar Talata, kamar yadda sanarwa ta nuna

- Marigay Alhaji Ahmed ya taba neman takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin inuwar tsohuwar jam'iyyar NRC

- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Fintiri, ya bayyana alhini tare da nuna bakin cikinsa akan rasuwar Alhaji Ahmed

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Umaru Fintiri, ya nuna juyayi tare da bayyana alhinin rasuwar jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Ahmed Song.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa marigayi Ahmed ya rasu ranar Talata, 12 ga watan Janairu, 2021, yana da shekaru 75 a duniya.

A sakonsa na ta'aziyya, gwamna Fintiri ya bayyana cewa rasuwar Alhaji Ahmed babban rashi ne da ya girgiza shi.

"Dan kishin kasa ne da ko kadan babu alamar gazawa a harkokinsa na gwagwarmaya," a cewar Fintiri.

Marigayi Alhaji Ahmed ya taba shugabantar kamfanin Sikari na Savannah wanda ke Numan a jihar Adamawa.

KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta

Kazalika, ya shugabanci kamfaninsa da ya kafa mai suna Rico Gado na sarrafa abincin dabbobi.

Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu
Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu
Asali: UGC

Tarihin rayuwarsa ya nuna cewa ya taba neman takarar kujerar gwamnan Adamawa a karkashin inuwar tsohuwar NRC, sannan ya taba rike mukamin mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin arewa maso gabas.

KARANTA: Fasto Yuana: Shekau yana cikin halin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

Kazalika, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, sun yi alhini tare da juyayin mutuwar wata mai kusanci da su, Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman.

Marigayiya Nafisatu mata ce wurin Laftanar Kanal IG Usman, dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.

A cikin sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gidan sarautar Adamawa, gwamnatin jiha da kuma jama'ar jihar baki daya.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai bayan ta sake sakin wani hotonta a dandalin sada zumunta.

Mabiyan jarumar a shafinta na Tuwita sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo.

Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata magana da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin fuskantar suka da tsangwama.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel