Yahaya Bello ya kamata ya zama Shugaban Najeriya na gaba inji PYB FRONTIERS
- Kungiyar PYB FRONTIERS ta fara bugawa Yahaya Bello gangar takarar a 2023
- Tace Gwamnan ya fi dacewa ya zama Shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari
- Daga dalilan magoya bayan Yahaya Bello shi ne ya kawo hadin kan kabilu a Kogi
Wata kungiya ta magoya bayan Yahaya Bello ta fito ta na jaddada kiranta na cewa gwamnan ya dace ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Wannan kungiya mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutane su marawa gwamnan na jihar Kogi baya domin ganin ya gaji Muhammadu Buhari.
Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kungiyar ta PYB FRONTIERS, Hans Mohammed ya na cewa sun fara kokarin ganin APC ta tsaida Yahaya Bello.
Hans Mohammed yake cewa gwamnan ya yi kokari a bangaren ilmin boko, kiwon lafiya, sha’anin tsaro da kuma yaki da annobar COVID-19 a jihar Kogi.
KU KARANTA: APC ta sha alwashin karbe wasu Jihohi daga hannun Jam’iyyun hamayya
A dalilin wannan ne kungiyar magoya bayan ta ke ganin Alhaji Yahaya Bello ya cancanci jam’iyyar APC ta ba shi tikitin takarar shugaban kasa.
A cewar Mohammed, gwamna Bello ya lashe kyaututtuka a gida da ketare a dalilin kokarin da yake yi na kare lafiya da dukiyar mutanen jihar Kogi.
Jaridar ta rahoto Mohammed yana cewa abin da ya dace shi ne gwamnan ya samu babbar kujera.
Kungiyar tace an ba gwamnan lambar yabo a bangaren ritita dukiyar al’umma, sannan ya taka rawar gani a harkar noma inda ya gina kamfanin casar shinkafa a Yagba.
KU KARANTA: Ana rikici tsakanin Sanatan Kaduna da Shugaban Majalisa
Bayan haka, kungiyar ta ce gwamnatin Bello ta kawo zaman lafiya tsakanin kabilun da ake da su a jihar Kogi, ta hanyar ba kowane bangare mukamai.
Duk a game da zaben na 2023, kun ji cewa jigon APC, Rochas Okorocha ya na kiran ‘Ya 'yan PDP da jam'iyyar APC duk su dunkule domin a gyara Najeriya.
Sanata Rochas Okorocha ya bayyana haka ne bayan gwamnan Ribas ya gayyaci jagoran APC domin ya kaddamar da wasu ayyuka da aka yi.
Okorocha ya ce Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng