Aminu Shagali ya roki Yusuf Zailani da Uba Sani suyi sulhu a Jihar Kaduna

Aminu Shagali ya roki Yusuf Zailani da Uba Sani suyi sulhu a Jihar Kaduna

- Aminu Shagali yayi tir da sabanin Magajinsa Yusuf Zailani da Uba Sani

- Shagali yace rigimar ‘Yan siyasar zata iya taba jam’iyya a jihar Kaduna

- Tsohon shugaban majalisar Jihar yace bai kamata a rika rigingimu ba

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Aminu Shagali ya yi tir da rikicin da ake yi tsakanin Uba Sani da Yusuf Zailani.

Jaridar The Nation ta rahoto Aminu Shagali yana cewa rigimar shugaban majalisar da Sanatan na Kaduna za ta iya shafan APC a zaben 2023.

Aminu Shagali mai wakiltar mazabar Sabon Gari a majalisar jihar Kaduna, ya yi kira ga manyan ‘yan siyasar su daina rikici, su hada-kansu.

‘Dan siyasar ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Kaduna, yace bai kamata rikicin gida ya bata masu gwamnati ba.

KU KARANTA: Kotu ta yi fatali da nasarar da ‘Dan Majalisar PDP ya samu a kan APC

‘Dan majalisar ya yi kira ga abokan siyasar na sa a jam’iyyar APC mai mulki su hakura da sabaninsu, suyi aiki da gwamnatin Nasir El-Rufai.

“Sam babu bukatar sanatan da shugaban majalisa su rika rigima a kan wani abu” A cewar Shagali.

Rt. Hon. Shagali yace: “Abin da Sanata Uba Sani yayi a ofis zuwa yanzu, ba a taba samun wani Sanatan Kaduna ta tsakiya da yayi wannan aiki ba.”

Tsohon shugaban majalisar yace: “Shugaban majalisa, Yusuf Zailani, ya fahimci cewa shugabanci hadin-kai ne. Babu bukatar su rika samun rikici.”

KU KARANTA: Manyan Yarbawa sun kai kujerar Shugaban kasa zuwa Kudu a 2023

Aminu A. Shagali Hoto: www.legit.ng/1243361-39-year-lawmaker-elected-kaduna-speaker.html
Aminu Shagali ya roki Yusuf Zailani da Uba Sani suyi sulhu a Jihar Kaduna
Source: UGC

A matsayinsa na ‘dan majalisa kuma tsohon shugaba, yace rikicin da ake yi, yana damunsa, yace na-kusa da gwamnan na neman kawo masa matsala.

A kudancin Najeriya labari ya zo mana cewa wasu tsageru sun kai wa Sanata mai wakiltar yankin Osun ta yamma majalisar dattawan tarayya hari.

Sanata Adelere Oriolowa ya bayyana wannan a shafin sa na Facebook a karshen makon nan.

Wani mai taimakawa Sanatan, Adams Adedimeji, ya tabbatar da faruwar wannan lamarin, ya ce Sanatan aka shirya kashewa, amma ba iya yin nasara ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel