Okorocha: Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara

Okorocha: Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara

- Rochas Okorocha ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan Ribas ya yi

- Tsohon gwamnan yace akwai bakaken wake a jam’iyyun PDP da ma APC

- Sanatan yayi kira ga mutanen kirki su hadu domin kawo gyara a Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya na kiran a samu hadin gambizar ‘yan siyasa da za su ceto kasar nan daga halin da ta samu kanta.

Jaridar Punch ta rahoto Sanata Rochas Okorocha yana wannan kira a lokacin da ya kaddamar da sabon titin Rumuche/Rumuakunde/Ohna Awuse a jihar Ribas.

A ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2020, Sanatan na yammacin jihar Imo ya ziyarci Ribas, ya bude sabuwar hanyar da gwamna Nyesom Wike ya yi.

Rochas Okorocha ya ba masu kishin Najeriya shawara su daina magiya, su hada-kai, su ceto jama'a.

KU KARANTA: Shugabar Majalisa ta bukaci a sauke Trump ko Majalisa ta tsige shi

Okorocha yake cewa a wannan marra, akwai mutanen banza a jam’iyyar APC, haka zalika PDP mai adawa, don haka ya bukaci na kwaran su hada-kansu.

“Ina tunanin ya kamata mutanen kirkin da ke APC da PDP su hadu da nufin ceto Najeriya tare.”

Tsohon gwamnan yace ya na hangen yiwuwar hada kai da irinsu gwamna Wike na PDP. Amma ‘yan siyasar sun sha ban-bam da juna ta fuskar akidar siyasa.

Sanatan yace ba maganar jam’iyya ta kawo shi Ribas ba, sai kauna da abokantakar da ke tsakaninsa da Nyesom Wike wanda karfinta ya zarce zumuncin jam’iyya.

KU KARANTA: Garambawul 10 da Buhari ya yi wa tattalin arziki a sabuwar doka

Okorocha: Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara
Sanata Rochas Okorocha Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Ya ce: “Mu tattaro wadanda su ka san abin da su ke yi, mutanen kwarai. A maimakon mu rika kuka, mu hadu domin mu ga yadda Najeriya za ta cigaba.”

A ranar Litinin kun ji cewa APC ta sha alwashin karbe wasu Jihohi daga hannun Jam’iyyun hamayya.

A jihar Adamawa, kusoshin 'yan siyasa irinsu Abdulaziz Nyako sun dawo sun hada kai APC, sun za su kifar da gwamnatin PDP ta Amadu Fintiri 2023.

Haka zalika shugaban APC ya ce za su gwabza da APGA da PDP a zaben gwamnan Anambra da za ayi a bana. APC ta ce ta gaji da zama a kujerar fasinja a motar jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng