Trump: Muna shirin tsige Shugaban kasa idan ba za a sauke shi ba inji Pelosi

Trump: Muna shirin tsige Shugaban kasa idan ba za a sauke shi ba inji Pelosi

- Majalisar Wakilan Amurka za ta dauko maganar tsige Donald Trump

- Nancy Pelosi tace za su tsige Shugaban kasar idan har ba a sauke shi ba

- ‘Yan Majalisa sun fara tarayya a kan wannan bayan aika-aikan Capitol

Rahotanni daga Reuters sun bayyana cewa majalisar wakilan Amurka za fara shirin tsige shugaban kasa Donald Trump daga karagar mulki.

Shugabar majalisar Amurka, Nancy Pelosi, a wata takarda da ta aikawa ‘yan majalisa a yammacin Lahadi, ta bayyana wannan shirin da za ta fara yau.

Ana zargin shugaban kasa Donald Trump da tarin laifuffuka bayan ya tunzura magoya bayansa sun yi ta’adi har cikin majalisar wakilan Amurka.

Shugabar majalisar Amurka, Nancy Pelosi tace jagororin majalisar za su bijiro maganar tsige Donald Trump ta hannun mataimakinsa, Mike Pence.

KU KARANTA: An hana Trump amfani da Twitter

Idan haka ya gagara, majalisar za ta soma muhawarar tsige shugaban kasar dake shirin barin mulki.

“A kokarin kare tsarin mulki da damukaradiyyarmu, za mu yi gaggawa, domin wannan shugabar kasar barazane ne ga duka.” Inji Pelosi a wasikar.

Tun da aka yi wannan abu, Donald Trump bai ce komai ba, musamman bayan hana shi amfani da dandalin Twitter. France 24 ta fitar da wannan rahoto.

‘Yan jam’iyyar adawa ta Democrats, suna so a gurfanar da Trump a gaban kotu, idan aka yi haka, za a haramta masu neman kujera har abada a Amurka.

KU KARANTA: Biden da Harris sun lashe zabe - Majalisa

Trump: Muna shirin tsige Shugaban kasa idan ba za a sauke shi ba inji Pelosi
Donald Trump Hoto: www.france24.com/en
Asali: UGC

‘Ya ‘yan jam’iyyarsu Trump irinsu Sanata Pat Toomey, Sanata Ben Sasse da Lisa Murkowski suna goyon bayan wannan yunkuri, ko shugaban ya yi murabus.

A ranar Laraba ne mataimakin Trump watau Mike Pence ya bar Shugaban kasa a tsaka mai wuya, ya tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben da aka yi.

Wasu mukarrabai suna ta barin gwamnatin Trump a sakamakon ta’adin da aka yi a majalisar wakilai lokacin da ake neman tabbatar da nasarar zaben 2020.

Gungun masoyan shugaba mai shirin barin-gado, Donald Trump sun nemi su kawo matsala a Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel