‘Finance Act’ ya kawo saukin aika kudi a banki da rahusar shigo da motoci a 2020

‘Finance Act’ ya kawo saukin aika kudi a banki da rahusar shigo da motoci a 2020

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kudirin Finance Act 2020

- Wannan kudiri da ya zama doka zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya

- Gwamnati ta rage wasu haraji da ta saba karba a da daga shekarar nan

Kudirin tattalin arziki na shekarar 2020, ya zo da sababbin manufofi da ake sa ran za su jawowa Najeriya kudin shiga tare da zabubar da tattalin kasar.

Jaridar The Cable ta tattaro wasu daga cikin amfanun wannan sabuwar doka aka kawo:

1. Motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motoci 5% daga 35%.

2. Babu haraji a kan duk ma’aikatan da albashinsu bai wuce N30, 000 ba.

3. An daina cire wani kaso da sunan kudin hatimi idan aka aika kudi a banki. Wanda aka aikawa kudin da suka kai akalla N10, 000 ne zai biya N50.

KU KARANTA: Dangote ya gangaro daga Attajirin Duniya na 106, dukiyarsa ta dawo $17.5b

4. An rage kudin harajin da ake karba a kan kananan kamfanonin da jarinsu bai kai Naira miliyan 25 ba.

5. Gwamnati za ta karbi aron kudin da aka manta da su a cikin banki kafin wanda ya mallake su ya dawo kansu.

6. Babu VAT a kan abincin dabbobi, kayan aikin gona jiragen sama na kasuwanci da sauran kayan jirgi. Haka zalika babu VAT a kan kudin tafiya a jirgi. Gwamnati ta cire VAT a kan filaye da gidajen da aka saida.

7. Za a rika karbar haraji a ribar da aka samu daga gudumuwa ko kyauta da gwamnati ta bada.

8. An rage mafi karancin harajin da ake karba a hannun kamfanoni daga 0.5% zuwa 0.25%.

‘Finance Act’ ya kawo saukin aika kudi a banki da rahusar shigo da motoci a 2020
Shugaban Najeriya Hoto: Twitter Daga: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Manyan Attajiran Duniya da irin tarin dukiyar da suka mallaka

9. Kamfanonin ketare za su bukaci lambar TIN, kuma za su rika biyan haraji.

10. Za a dauke biyan haraji daga kamfaonin da ke aikin gona da noman dabbobi da kifi.

Kun ji wani bawan Allah da ya bada labarin yadda wani abokinsa ya taimaka masa da jari da shago domin fara neman kudi, yanzu kasuwancinsa ya bunkasa.

Wannan matashi mai zuciyar nema ya mallaki shago yanzu, bayan ya fara ne daga karbar bashin jarin N10, 000 a hannun wannan abokinsa da ya taimaka masa.

Sir Abba Farmer yace yanzu a shagonsa akwai magani guda wanda kudinsa ya haura N10, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng