“Zamu karbe Jihar Adamawa da Anambra a zabukan 2021, 2023” Inji APC

“Zamu karbe Jihar Adamawa da Anambra a zabukan 2021, 2023” Inji APC

-APC ta fara shirin karbe Jihar Adamawa daga hannun jam’iyyar APGA

-Jam’iyyar ta yarda ba ta tabuka abin kwarai a zabukan 2019 da 2017 ba

-Su ma wadanda suka dawo APC a Adamawa sun fara sa ido a kan 2023

‘Ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Adamawa sun karbi wasu manyan ‘yan siyasa da ake ji da su wadanda suka dawo cikin tafiyarsu.

Jaridar The Nation ta ce wadannan ‘yan siyasa sun ce za su bada gudumuwa wajen tika jam’iyyar PDP mai mulkin Adamawa da kasa a 2023.

‘Yan siyasar suna kan ra’ayin cewa sabanin da aka samu a 2019 ne ya yi sanadiyyar da jam’iyyar APC ta sha kashi a zaben da ya wuce.

Sanata Abdulaziz Murtala Nyako yana cikin wadanda suka dawo tafiyar APC. Nyako ya bar jam’iyyar ADC da ya jagoranta a 2019.

KU KARANTA: Ana yi wa Sanatan APC bore a Kaduna

Abdulaziz Nyako ya ce: “Daga yau mu cikakkun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne. Dole mu yi amfani da wannan haduwa da aka sake yi, mu fito da ‘yan takarar da suka cancanta a 2023.”

Sauran wadanda suka bar jam’iyyun adawa da PDP suka koma APC sun hada da Sanata Elisha Ishaku Abbo da tsohon mataimakin gwamna Bala Ngillari

A jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya kuma, shugaban APC na rikon kwarya, Basil Ejidike, yace sun gaji da zama ‘yan adawa.

Da yake magana wajen wani taron jam’iyyar APC a garin Akwa, Mista Basil Ejidike ya ce sun shirya karbe mulkin Adamawa daga hannun APGA.

“Zamu karbe Jihar Adamawa da Anambra a zabukan 2021, 2023” Inji APC
Shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni Hoto: Premium Times Daga: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun dura Kauyen Zamfara, sun hallaka mutane

George Moghalu bai halarci taron da ya samu halartar Andy Uba, Tony Nwoye da Chris Ngige, wanda ya koka da yadda ba a yi wa ‘ya ‘yan jam’iyya sakayya.

Tony Nwoye da yake jawabi, yace jam’iyyar APC ba ta tabuka wani abin kwarai a zaben 2017 ba, yace mun gaza samun ko da kujerar majalisa guda.

Idan muka koma siyasar jihar Kaduna za mu ji cewa manyan jam'iyyar APC sun fara koka da rigimar Rt. Hon. Yusuf Zailani da Sanata Uba Sani.

Aminu Shagali ya shiga cikin maganar, ya roki jiga-jigan APC dake rikici su yi sulhu.

Tsohon shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon Aminu Shagali y ace sabanin da ake samu zai iya yi wa jam'iyyar APC lahani a jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel