An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000

An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000

- Kotu ta daure wani malami a kasar Turkiyya mai da'awa tare da mata zagaye dashi

- Kotun ta yanke masa hukuncin shekaru fiye da 1,000 a gidan yari

- Wanda aka dauren sananne ne a telebijin mata na rawa a gabansa

Wani masanin addinin Islama mai yada shirye-shiryensa a telebijin wanda yake kewaye kansa da mata sanye da kayan badala a talabijin, an daure shi sama da shekaru 1,000 a ranar Litinin saboda aikata laifuka na lalata, in ji kafofin watsa labarai na cikin gida, Channels Tv ta ruwaito.

Adnan Oktar ya yi wa'azin ra'ayoyi masu tsauri, yayin da matan da ya kira "kittens" dinsa - wadanda da yawa daga cikinsu sun bayyana cewa an yi musu tiyatar filastic - suna rawa a kusa da shi a gidan talabijin.

An tsare shi Adnan Oktar, dan shekaru 64 a watan Yunin 2018 a matsayin wani bangare na fatattakar kungiyarsa da sashin aikata laifuka na kudi na ‘yan sandan Istanbul.

An yanke masa hukuncin daurin shekara 1,075 kan laifuka da suka hada da cin zarafin mata, lalata da kananan yara, zamba, da yunkurin leken asiri na siyasa da soja, gidan talabijin na NTV mai zaman kansa ya ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000
An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000 Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

An gurfanar da wasu mutane 236 da ake zargi a gaban shari’ar, 78 daga cikinsu suna hannun hukuma, a cewar kamfanin dillacin labarai na Anadolu.

Jawaban sun gabatar da cikakkun bayanai na karya da kuma munanan laifuka na lalata da mata.

Oktar ya fadawa alkalin da ke sauraron karar a watan Disamba cewa yana da kusan 'yan mata 1,000.

“Akwai malalar kauna a zuciyata ga mata. Kauna halin mutum ne. Kauna ce ta Musulmi,” in ji shi a wani sauraren karar a watan Oktoba.

Ya kara da cewa a wani lokaci: "Ina da karfi sosai."

Oktar ya fara zuwa bainar jama'a ne a cikin shekarun 1990 lokacin da yake shugaban wata kungiyar darika da ta afka cikin badakalar jima'i da yawa.

Tashar talabijin dinsa ta A9 da ke intanet ta fara watsa shirye-shirye a shekarar 2011, inda ta jawo masa tofin Allah tsine daga shugabannin addinan Turkiyya.

Daya daga cikin matan da ake yi wa shari’ar, wacce aka bayyana sunanta da CC, ta fada wa kotun cewa Oktar ya sha yin lalata da ita da wasu mata.

Wasu daga cikin matan da ya yi wa fyade an tilasta musu shan kwayoyin hana daukar ciki, kamar yadda CC ta shaida wa kotun.

Da aka tambaye shi game da kwayoyin hana daukar ciki 69,000 da ‘yan sanda suka gano a gidansa, Oktar ya ce an yi amfani da su ne wajen magance cututtukan fata da kuma rashin bin al’ada.

KU KARANTA: Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata

Ya kuma yi watsi da duk wata alaka da wata kungiya karkashin jagorancin mai wa’azin musulinci Fethullah Gulen da ke Amurka, wanda hukumomin Turkiyya ke zargi da kitsa yunkurin juyin mulki a shekarar 2016.

Oktar yayi imani da samuwar mahalicci wanda yayi watsi da akidar Darwin ta juyin halitta kuma ya rubuta littafi mai shafi 770 mai suna "The Atlas of Creation" karkashin sunan alkalami, Harun Yahya.

A wani labarin, Wata Babbar Kotun Majistare da ke zaune a Wuse Zone 2, Abuja ta ba da belin mai gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore a kan kudi Naira miliyan 20.

Wanda ake kara na biyu kuma ya bayar da belin su a kan kudi Naira miliyan daya da kuma mutum daya da zai tsaya musu.

Babban alkalin kotun, Mabel Segun-Bello yayin da take yanke hukunci kan neman belin a ranar Litinin ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel