Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Amurka ta amince da nasarar Joe Biden kan Donald Trump
- Bayan rikita-rikitan da ya faru ranar Laraba, majalisar dokokin Amurka ta samu zama
- Yan majalisar wakilai da na dattijai sun kada kuri'a don rattaba hannu kan sakamakon zabe
- Mataimakin Trump, wanda shine shugaban majalisar ya watsa masa kasa a ido
Majalisar dokokin Amurka ta tabbatar da nasarar Joe R Biden Jr a matsayin zababben shugaban kasa bayan nasara kan Donald Trump.
Kidayar kuri'un jihar Vermont ta baiwa Joe Biden adadin kuri'un Electoral College 279 da yake bukata tare da mataimakiyarsa, Kamala Harris.
Majalisar datawar Amurka da na wakilai sun yi watsi da bukatar hana Joe Biden kuri'un Georgia da Pennsylvania.
Bayan haka yan majalisar jam'iyyar Republican sun nuna rashin amincewarsu da kuri'un jihar Arizona, Nevada, da Michigan, amma duka akayi watsi.
A karshe, majalisar ta sanar da cewa Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya samu jimmilar kuri'un Electoral College 306, yayinda Donald Trump na jam'iyyar Republican ya samu jimillar kuri'ar 232.
Hakazalika, Kamala Harrisa, mataimakiyar Joe Biden ta jam'iyyar Democrat ta samu kuri'u 306, yayinda Mike Pence mataimakin Donald Trump na jam'iyyar Republican ya samu jimillar kuri'ar 232.
KU KARANTA: Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka
KU DUBA: Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani
Tabbatar da nasarsa ya biyo bayan zanga-zangar da masoya Trump sukayi a ranar Laraba.
Masoya shugaban kasan Amurka, Donald Trump, sun fasa cikin majalisar dokokin Amurka kuma hakan ya sa an dakatar da zaman rattaba hannu don tabbatar da Joe Biden matsayin zababben shugaban kasar.
Hakan ya tilasta kwashe jama'an dake cikin ofishohin majalisar gudun kada a samu matsala.
Sakamakon haka an yi rashin rayuka hudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng