Zanga-zanga: An bijiro shirin tsige Donald Trump, Hadiman Shugaban Amurka suna ajiye mukamansu

Zanga-zanga: An bijiro shirin tsige Donald Trump, Hadiman Shugaban Amurka suna ajiye mukamansu

- Jami’in Gwamnatin Amurka ya yi murabus a sakamakon harin Capitol

- An fara kiran a tunbuke Donald Trump daga kujerar shugaban Amurka

- Ana zargin kalaman Trump ne suka tunzura masoyansa wajen yin ta’adi

A daren yau Alhamis ne aka samu wasu bata-gari da ake zargin magoya bayan Donald Trump ne su ka nemi su kawo fitina a majalisar Amurka.

Wadannan masoya na shugaba mai shirin barin-gado, Donald Trump sun nemi su kawo matsala yayin da ake tabbatar da zaben 2020 da aka yi.

Wannan rigima da ta barke ta yi sanadiyyar da mataimakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Mr. Matt Pottinger, ya yi murabus.

Pottinger ya sauka daga kujerarsa, ya na tir da abin da shugaban kasar ya yi. Ita ma hadimar uwargidar Trump, Stephanie Grisham ta ajiye aiki.

KU KARANTA: An rufe shafukan Shugaban Amurka Trump

Zuwa yanzu manyan hadiman shugaban kasar Amurkan kamar NSA Robert O'Brien da Chris Liddell su na tunanin rubuta takardar barin aiki.

Shi kuma mataimakin shugaban kasa Mike Pence, ya jagoranci zaman majalisar wakilai, inda ya tabbatar da duk kuri’un da aka kada a zaben 2020.

A wannan zama da Mike Pence ya jagoranta, ba a karbi ikirarin da ake yi na magudin zabe ba.

Jaridar The Times ta Ingila ta fitar da rahoto cewa jama’a sun fara kiran ayi amfani da dokar kasa, a tuntube shugaba Donald Trump daga kan mulki.

KU KARANTA: Majalisa ta yarda Biden da Harris sun ci zabe

Zanga-zanga: An bijiro shirin tsige Donald Trump, Hadiman Shugaban Amurka suna ajiye mukamansu
Majalisar Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kiran da ake yi na tsige shugaban kasar ya na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kwanaki kadan suka rage masa ya bar ofis, ya ba Joe Biden mulki.

A Najeriya kuma kwanakin baya aka ji cewa guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai inda PDP ta ke rasa 'ya 'yanta zuwa APC.

Wani rahoto ya nuna cewa akwai yiwuwar samun karin wasu 'yan majalisar da zasu koma APC.

Sauyin shekar ba zai rasa nasaba da shirin zaben shekarar 2023 ba wanda ya sa irinsu Elisha Abbo. Yakub Dogara, da Ali Datti Yako su ka bar PDP ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng