'Yan bindiga sun kai wa Sanata hari a Osun yayin taro a mazaɓarsa
- Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai wa sanata mai wakiltar Osun West a majalisar dattawa hari
- Sanata Adelere Oriolowa ya bayyana ta shafin sa na Facebook cewa harin yunkurin kashe shi ne kai tsaye
- Babbar mataimakin ya ce an samu nasarar cetar mai gidansa cikin koshin lafiya kuma yanzu haka ya na gidansa da ke Osogbo
An kawo wa sanata mai wakiltar Osun West a majalisar dattawa, Adelere Oriolowa dauki daga wajen taron mazabar sa da ya gudana a Ikire, Jihar Osun, ranar Lahadi bayan wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai masa hari.
Babban mai taimakawa sanatan, Adams Adedimeji, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilan mu, ya ce sanatan aka shirya kashewa.
DUBA WANNAN: Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiyya
Ya ce sanatan ya je taron mazabun sa a garin Ikire da ke karamar hukumar Irewole a jihar Osun, wanda ke karkashin inda ya ke wakilta.
Oriolowa ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa yan bindigar sun yi yunkurin kashe shi.
Ya rubuta, "yanzu na tsira daga wani yunkurin kashe ni da aka shirya ni da tawaga ta. Mun gode, muna raye cikin koshin lafiya.
"Allah ne mai taimakona, mai kare ni kuma garkuwa na, bana tsaron ko wane sharri."
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi
Adedimeji, ya tabbatar wa da wakilinmu cewa an ceto ceci mai gidan sa lafiya kuma yanzu haka yana Osogbo, babban birnin jihar lokacin hada wannan rahoto.
Ya ce, "an riga an fara taron lokacin da maharan suka bullo. Sun faffasa gilashin motar sa amma yanzu yana lafiya. Yanzu haka yana gidan sa da ke Osogbo."
A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.
A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.
Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng