Kotu ta soki hukuncin da Alkali ya zartar a shari’ar zaben kujerar Sanatan Bayelsa

Kotu ta soki hukuncin da Alkali ya zartar a shari’ar zaben kujerar Sanatan Bayelsa

- Har yanzu ba a kammala shari’ar zaben kujerar Sanatan Bayelsa ta yamma ba

- Kotun daukaka kara ta yi watsi da nasarar da Sanata Seriake Dickson ya samu

- Alkalan kotun daukaka kara sun bukaci a sake shari’a a kan korafin da aka kai

Kotun daukaka kara na Fatakwal, jihar Ribas, ta yanke hukunci cewa Sanata Seriake Dickson yana da tambayar da zai amsa a gaban Alkali.

Babban kotun kasar ta fara yanke hukunci a shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan na Bayelsa, inda ake neman soke takarar majalisar da ya yi.

A zaman da Alkalan kotun daukaka kara su kayi a karkashin Mai shari’a U. Onyemenam, an soki hukuncin da Alkalin babban kotun tarayya ya yi.

The Nation tace Onyemenam da abokan aikinsa sun bukaci a maida karar da aka shigar da Dickson wajen wani Alkalin kotun tarayya daban.

KU KARANTA: Duk da COVID-19, Kwatsam ta nemo kudin da ya zarce na 2019 a 2020

Alkalan kotun sun zartar da cewa bai dace ace kotun tarayya ta yi watsi da wannan shari’a dake gabanta ba, kotun ta ce Alkalin ya tafka kuskure.

Wanda yake karar tsohon gwamnan, Owoupele Eneoriekumoh, ya bukaci ayi fatali da hukuncin babban kotun tarayya na Yenogoa, jihar Bayelsa.

Eneoriekumoh ya shigar da kara ne ta hannun lauyoyinsa, Pius Danba Pius da Ebikebuna Augustine Aluzu, kuma ya fara samun nasara a kotu.

Manyan Alkalan sun saurari korafin Danba Pius da Ebikebuna Augustine Aluzu, suka ce bai kamata J. Inyang ya yi watsi da karar da aka kai ba.

Kotu ta soki hukuncin da Alkali ya zartar a shari’ar zaben kujerar Sanatan Bayelsa
Sanatan Bayelsa ta Yamma Seriakedickson Hoto: guardian.ng/tag/seriake-dickson
Asali: UGC

KU KARANTA: Manyan Yarbawa zasu matsawa APC lamba ta kai takara yankin Kudu

Da wannan danyen hukunci da aka yi, za a koma karamin kotun domin sauraron karar daga farko, a karkashin wani sabon Alkali daban da Inyang.

A shekarar bara kun ji cewa jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa na Bayelsa ta yamma wanda hukumar INEC ta gudanar.

Tsohon Gwamna Seriake Dickson ya yi galaba kan Peremobowei Ebebi na jam'iyyar APC.

Daga baya an samu irinsu Owoupele Eneoriekumoh suna kalubalantar wannan zabe da wasu jami’an tsaro su kayi hadarin kwale-kwale a dalilinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel