Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutane, sun tsere da dabbobi a Kauyen Dada

Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutane, sun tsere da dabbobi a Kauyen Dada

-An bar Jama’a da kirga tarin gawa bayan harin da aka kai wa Zamfara

-Rahotanni sun tabbatar da cewa an hallaka mutane a harin da aka kai

-‘Yan bindigan sun aukawa kauyen ne dauke da makamai a kan babura

Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun shiga wani kauye da ake kira Dada, jihar Zamfara sun hallaka mutane a ranar Juma’ar nan.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, ta ce an kashe mutane da-dama, sannan an saci dabbobi a wannan harin.

Mazauna wannan kauyen sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shigo Dada ne a kan babura, dauke da makamai suna harbi.

Wadannan miyagu sun budawa jama’a wuta, sannan suka toshe hanyoyin da za a bi a tsere.

KU KARANTA: Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Birnin Gwari

“Miyagun ‘yan bindigan sun zo ne a kan babura, suka fadawa mutane su zauna a cikin gidajensu. Wasu sun mutu suna kokarin tserewa harin.”

“Yanzu haka dana ke magana, ba zan iya fada maka adadin mutanen da aka kashe ba. ‘Yan bindigan sun gudu bayan zuwa jami’an tsaro.”

Majiyar ta kara da shaidawa ‘yan jarida cewa ana cigaba da binciken gawar wadanda aka hallaka.

Wani mai suna Ali Shuaibu ya ce mutane sun shiga daji suna neman gawar wadanda suka mutu. Ya ce: “Muna ta kirga ta’adin da aka yi mana.”

KU KARANTA: An yi rikici tsakanin Sojoji da Direbobi, mutum 5 sun mutu

Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutane, sun tsere da dabbobi a Kauyen Dada
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Daga: Twitter Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Jaridar tace tayi yunkurin tuntubar jami’an ‘yan sanda, amma ba ayi nasarar cin ma kakakin rundunar na Zamfara, SP Muhammad Shehu ba.

A bayan kun ji an kubuto da mutum 70 da suka fada hannun masu garkuwa da mutane a Katsina.

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa kungiyar Miyetti Allah ta hada-kai da Jami’an tsaro wajen ceto wadannan Bayin Allah.

Tun da aka gano daliban da aka sace kwanaki a garin Kankara, gwamnatin Katsina ta gano sabuwar dabarar ceto mutanen da ake daukewa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel