Yan bindiga sun tsere yayinda sojoji suka tarwatsa mabuyarsu a Kaduna

Yan bindiga sun tsere yayinda sojoji suka tarwatsa mabuyarsu a Kaduna

- Dakarun sojoji suna ragargaji yan bindiga a mabuyarsu da ke yankin Birnin Gwari, jihar Kaduna

- Jirgin yakin sojin sama ne ya kai masu farmakin a Sani Maichuku, Alhaji Chorki, Sangeku, Zabiya, Dutsen Magaji, da Kotonkoro a jihar

- Wasu daga cikin yan ta'addan sun ci na kare a yayin kakkaban

Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun kakkabe yan bindiga daga mabuyarsu a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

A cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, an gudanar da ayyukan sojoji a Sani Maichuku, Alhaji Chorki, Sangeku, Zabiya, Dutsen Magaji, da Kotonkoro a jihar.

A wata sanarwa, Aruwan ya ce wasu daga cikin miyagun sun tsere a yayin kakkaban.

Yan bindiga sun tsere yayinda sojoji suka tarwatsa mabuyarsu a Kaduna
Yan bindiga sun tsere yayinda sojoji suka tarwatsa mabuyarsu a Kaduna Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

“A ci gaba da aikin kakkaba da ake yi don gano mabuyar yan bindiga, rundunar sojin sama sun kaddamar da hari a mabuyarsu da ke karamar hukumar Birnin Gwari,” in ji shi.

“A bisa ga jawabin aikin da aka gabatarwa gwamnatin jihar Kaduna, ya nuna cewa an aiwatar da aikin ne a kan Sani Maichuku, Alhaji Chorki, Sangeku, Zabiya, Dutsen Magaji, Kotonkoro da sauran mazauninsu.

KU KARANTA KUMA: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna

“A Sani Maichuku, an gano mazaunin yan bindiga da dama, sannan aka fafata da su yayinda wasu yan bindiga suka yi yunkurin tserewa kan babura uku.

“Hakazalika, a Alhaji Chokri, an gano yan bindiga a kan babura biyar da dabbobi, sannan jirgin yakin ya yi nasarar kashe su. An ci gaba da zantawa da dakarun sojin kasa musamman a Zabiya da Gwaska; ba a gano kowani abun zargi ba a yankunan.”

Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya yaba ma rundunar soji kan ayyukan wanda yace yayi sanadiyar hana yan bindiga katabus din yin wani abu.

Gwamnan ya shawarci mazauna yankunan da su ba jami’an tsaro hadin kai a aikinsu.

KU KARANTA KUMA: Mutum 5 sun rasa ransu yayinda aka yi karo tsakanin sojoji da direbobin haya a Kwara

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da lokacin da za a kawo karshen yaki da Boko Haram da yan bindiga a Najeriya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaban kasar, wanda ya bayyana haka a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, ya ce za a kammala yaki da ta’addanci a karshen shekarar nan ya 2021.

Legit.ng ta tattaro cewa ya yi kira ga taya rundunar sojin saman Najeriya da addu’a domin su samu damar kawo karshen abunda suke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel