Mutum 5 sun rasa ransu yayinda aka yi karo tsakanin sojoji da direbobin haya a Kwara

Mutum 5 sun rasa ransu yayinda aka yi karo tsakanin sojoji da direbobin haya a Kwara

- An yi karo tsakanin sojoji da direbobin mota a yankin Ilesha-Babura da ke karamar hukumar Baruten da ke jihar Kwara

- Mutum biyar sun rasa ransu a karon sakamakon harbinsu da ake zargin sojojin da yi

- An kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti domin samun kulawa

Akalla yan farar hula biyar ne suka rasa ransu a Ilesha-Baruba, karamar hukumar Baruten a ke jihar Kwara biyo bayan wani karo tsakanin wasu sojoji a direbobin kasuwa.

A cewar majiyoyi, rikicin ya afku ne a yammacin ranar Juma’a sakamakon wani sabani tsakanin sojoji a suka sanya shingaye a hanyar titin Ilesha-Baruba/Chikanda a kuma direbobin motar haya da ke bin hanyan.

Majiyoyi sun fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa wani direba, wanda ya fito daga kasuwar Sinawu da ke yankin, yaki biya N200 da jami’an da ke hanyar suka bukaci ya biya.

Mutum 5 sun rasa ransu yayinda aka yi karo tsakanin sojoji da direbobin haya a Kwara
Mutum 5 sun rasa ransu yayinda aka yi karo tsakanin sojoji da direbobin haya a Kwara Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

An tattaro cewa direban ya fada masu cewa ya riga ya biya kudin da safe.

KU KARANTA KUMA: FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA

Rahoton ya nuna cewa rashin biyan kudin da direban yaki yi shine ya sa jami’an suka mare shi tare da sanya shi yin tsallen kwado.

A cewar majiyoyi an kuma kwace masa abun hawansa.

Daga bisani sai direban ya bar wajen sannan ya kai korafi wajen jami’an kungiyar sufuri a yankin.

Sai mambobin kungiyar suka bi direban da nufin yi wa sojojin magana a madadinsa.

Sai dai hakan ya haddasa zazzafa cece-kuce, lamarin da ya kai ga harbin wasu direbobi inda aka yi zargin cewa a nan take uku suka mutu sannan biyu suka mutu daga baya sakamakon raunin harbi.

Daya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa an dauki gawawwakin mamatan zuwa dakin ajiyar gawa a Saki, jihar Oyo, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa wasu da suka ji munanan rauni na nan suna samun kulawa a wani asibiti da ke Saki yayinda aka dauki wasu zuwa wajen masu maganin gargajiya a kauyen Kenu don cire harsashi daga cikinsu.

KU KARANTA KUMA: Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa kan lamarin harbin, SP Ajayi Okasanmi, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kwara ya tabbatar da rikicin tsakanin sojoji da direbobin.

Sai dai, Okasanmi ya bayyana cewa rundunar bata riga ta tabbatar da adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikka ta ba inda ya kara da cewa za a gudanar da bincike don sanin gaskiya.

Ya kuma ce tuni kwanciyar hankali ya dawo yankin da abun ya faru.

A wani labarin, mun ji cewa an halaka mutane uku yayin da wani daya ya samu rauni a lokacin da wasu mayakan ta'addanci da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a daren Laraba, majiyoyi suka sanar.

An gano cewa 'yan ta'addan sun tsinkayi kauyen Ngunari kusa da Yankin Moromti wurin karfe 10:30 na dare a karamar hukumar Konduga inda suka kashe mutum uku. Abubakar Kulima jami'in tsaro ne daga cikin jami'an hadin guiwa na CJTF.

Ya ce maharan sun dinga harbe-harbe kuma sun yi awon gaba da dabbobi a kauyen, Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel