Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar

Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar

- Buhari ya kaddamar da cewa kashe kashe da garkuwa da mutane da ake yi zai zo karshe a Najeriya kafin karshen 2021

- Shugaban kasar ya fadi hakan a Abuja, babbar birnin tarayya, a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, bayan sallar Juma’a

- A cewarsa, zai tabbatar da ganin cewa an kare rayuka da dukiyoyin kowani dan Najeriya

Daga karshe Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da lokacin da za a kawo karshen yaki da Boko Haram da yan bindiga a Najeriya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaban kasar, wanda ya bayyana haka a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, ya ce za a kammala yaki da ta’addanci a karshen shekarar nan ya 2021.

Legit.ng ta tattaro cewa ya yi kira ga taya rundunar sojin saman Najeriya da addu’a domin su samu damar kawo karshen abunda suke yi.

Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar
Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Buhari wanda yayi magana a lokacin sallar Juma’a don tunawa da ranar rundunar soji a babbar birnin masallacin kasa, ya kuma bayar da tabbacin cewa “Wannan shekarar aiki ne da gama abunda muke yi.”

Ya ce:

“A wannan shekarar Za mu kawo karshen abunda muke yi; ku taya my da addu’an samun nasara.”

Ya bayyana cewa kasar Za ta ci gaba da tunawa da ayyukan jarumta da rundunar soji sannan Za ta ci gaba da addu’a ga wadanda suka mutu a yayin kare martabar kasar.

Buhari ya kuma bayar da tabbacin cewa za a kula da jin dadi da kwanciyar hankalin iyalan jaruman da suka mutu, sannan kuma wadanda ke raye za su samu kulawar gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari

A hudubarsa, babban limamin masallacin kasa, Mohammed Kabiru Adams, ya yi addu’a ga jaruman da suka rasa ransu.

Ya kuma yi addu’a don ganin karshen ta’addanci, fashi da makami da sauran laifukan da suka addabi kasar.

A wani labarin, mun ji cewa rayuka uku suka salwanta yayin da wani mutum daya ya samu rauni a sabon harin 'yan Boko Haram.

Mayakan ta'addancin sun kai hari kauyen Ngunari da ke kusa da garin Maiduguri na jihar Borno.

Bayan kashe mutum ukun, sun kwashe akuyoyi, kaji da raguna inda suka yi awon gaba da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel