Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna

Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna

- Dakarun sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga ta tudu da sama a Kaduna

- Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da halaka 'yan ta'addan

- Sojin sun kai samamen a garuruwan Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau da sauransu

'Yan bindiga masu tarin yawa sun cimma ajalinsu sakamakon samamen tudu da na jiragen yaki da soji suka kai musu a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a jihar Kaduna, Vanguard ta wallafa.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya ce dakarun sun tabbatar da samamen da suka kai a ranar Litinin a Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau, Fadama kanauta, Galadimawa, Kaya, Kidandan, Yadi, Dogon Dawa, Ngede Allah, Damari, Saulawa, Takama, Kuduru, Ungwan Yakoda babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"An ga 'yan bindiga a Yadi kuma an ragargaji yankin ta sama sannan an kashesu da yawansu," yace.

KU KARANTA: Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC

Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna
Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga ta jiragen yaki da tudu a jihar Kaduna. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

"Hakazalika, a titin da ya hada Kuduru da Ugwan Yako, an ga 'yan bindiga tare da shanun sata kuma an halaka su.

"Sauran yankunan da aka duba an ga lafiya kalau sannan dakarun tudu sun duba yankunan kuma babu 'yan bindigan," yace.

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna gamsuwarsa a kan nasarar da ake samu tare da jinjinawa dakarun a kan yadda suke kokarin ganin bayan 'yan bindiga.

Gwamnan ya yi kira ga 'yan jihar da su bada goyon baya ta hanyar bayyana duk wasu al'amuran 'yan bindigar ga jami'an tsaro

KU KARANTA: In har liyafar badala ta sa aka rushe otal, gidan dan El-Rufai ya dace a fara rushewa, Reno Omokri

A wani labari na daban, Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwasoo, dukkansu tsofaffin gwamnonin jihar Kano sun kasance tsoffin makiya a siyasance wadanda basu iya zama a inuwa daya ballantana a siyasa.

Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003 a lokacin da Kwankwaso yake neman zarcewa. Kwankwaso ya yi nasarar a 2011 inda ya kayar da Salihu Sagir Takai a zaben gwamnoni.

Kwankwaso ya sake nasara bayan Ganduje dan takararsa ya maka Takai dan takarar Shekarau da kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel