Seriake Dickson zai wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya doke APC

Seriake Dickson zai wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya doke APC

- Jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa na Bayelsa

- Tsohon Gwamna Seriake Dickson ya yi galaba kan Peremobowei Ebebi na APC

- Sakamakon wannan zabe, wasu jami’an tsaro sun mutu a hadarin kwale-kwale

Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson wanda ya tsaya wa jam’iyyar PDP takara a zaben Sanata na yankin yammacin jihar ya samu nasara.

Jaridar The Nation tace jam’iyyar PDP mai rike da jihar Bayelsa ta doke APC mai hamayya a zaben da aka yi domin cike guraben dake majalisa.

Kamar yadda hukumar INEC ta bada sanarwa a cikin karshen makon nan, Seriake Dickson ya samu kuri’a 115, 257, ya doke Peremobowei Ebebi da APC.

Mista Peremobowei Ebebi ya tashi da kuri’a 17,500 a wannan zabe na kujerar Bayelsa ta yamma a majalisar dattawa, ratar 97757 ke tsakanin jam’iyyun.

KU KARANTA: PDP ta fadi zaben Sanata a Filato, APC ta yi nasara

Da wannan nasara, jam’iyyar PDP maras rinjaye a majalisar tarayya, ta samu karin kujera daya.

Yayin da Seriake Dickson yayi gwamna tsakanin 2012 da 2020, Peremobowei Ebebi tsohon mataimakin gwamna ne kuma ya taba rike kujerar majalisa.

Ebebi yana wakiltar mazabar Ekeremor I a lokacin da majalisar dokokin Bayelsa ta tsige Diepreye Alamieyeseigha ta nada Goodluck Jonathan kan kujerar.

Channels TV tace wasu ‘yan sanda shida da aka tura aikin zabe sun mutu a yankin Ijaw, Bayelsa, jami’an sun rasu ne a sanadiyyar hadarin jirgin ruwa.

KU KARANTA: Lokacin da Buhari ya zargi Jonathan da hannu a rikicin Boko Haram

Seriake Dickson zai wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya doke APC
Dan takarar APC, Peremobowei Ebebi da Seriake Dickson Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

A jiya mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Bayelsa, Asinim Butswat, yace jirgin ruwa ya kife da jami’ansu 11 a ranar Asabar, amma an ceto biyar da ransu.

Kwana-kwanan nan kuka ji cewa 'yan bindiga sun hallaka wani jami'in dan sanda yayin da suka kai hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson.

Idan ba ku manta ba wannan mugun lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba a gidan tsohon gwamnan da ke Toru-Orua a yankin, Sagbama.

Hakan na zuwa ne watanni bayan Seriake Dickson ya bar kan kujerar gwamna da yake kai tun 2012.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel