Mun samu N1, 562, 115, 419, 216.32 a shekarar da ta wuce inji Hukumar NCS
- ‘Yan Kwastam sun bada mamaki, sun samu kudin da ya zarce abin da aka yi hari
- Hukumar da ke kula da fasa-kaurin tace ta tatsi N1,562,115,419,216 a shekarar 2020
- Wannan kudi da aka samu ya zarce abin da aka yi hari da kusan Naira biliyan 200
A ranar Laraba, 6 ga watan Junairu, 2020, jami’an hukumar kwastam ta kasa ta bayyana adadin kudin da ta tatsowa Najeriya a shekarar da ta gabata.
Hukumar da ke yaki da fasa kauri a Najeriya ta ce ta samu N1,562,115,419,216.32 a shekarar 2020.
Wannan makudan kudi da hukumar kwastam ta samu ya haura lissafin hasashen N1,380,765,353,462 da aka yi a farkon shekarar da ta wuce.
Punch ta ce wannan kudi da aka samu a bara ya zarce N1,342,006,918,504.55 da aka iya tatsa a 2019.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Bello da Buni
Shugaban hukumar yaki da fasa-kaurin, Hameed Ali ya ce sun yi nasarar samun wadannan makudan kudi ne saboda jajircewa da matakan da aka dauka.
A jawabin da NCS ta fitar daga bakin mai magana da yawunta, Joseph Attah, ya ce ya shigo da dabarun zamani a lokacin da ake ta fama da annobar COVID-19.
Joseph Attah ya ce kudin da hukumar kwastam ta ke samu ya na yin sama duk shekara saboda irin gyara-gyaren da ake kawowa wajen aikin yaki da fasa-kauri.
Ya ce: “Kafin a rufe iyakoki a Agustan 2019, abin da hukumar NCS ta ke samu ya na tsakanin N4bn da N5bn, amma yanzu mu na samun N5b zuwa N9bn kullum.”
KU KARANTA: Minista ya ce Gwamnatin Tarayya za ta inganta alakarta da Sin
Ali ya bayyana shirin da CBN ta ke yi na ganin an kafa na’urorin da za a rika sa ido a kan duk abin da ke faruwa a iyakokin kasar domin maganin masu barna.
A makon nan kun ji bayanin irin tasirin annobar COVID-19 da rufe iyakoki a kan tattalin arzikin Najeriya wanda har ta kai ga ya durkushi a karshen 2020.
Masana sun ce cire tallafin mai da karin kudin wutar lantarki da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a shekarar 2020, ya jefa tattalin Najeriya a halin ha’ula’i.
Annobar Coronavirus da matakan da gwamnati ta rika dauka su ka haddasa tsadar kayan abinci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng