Zugar mambobin PDP ta dunguma zuwa jam'iyyar APC a Zamfara

Zugar mambobin PDP ta dunguma zuwa jam'iyyar APC a Zamfara

- Dubun dubatar mambobin jam'iyyar PDP sun yi kaura zuwa jam'iyyar APC a garin Kauran Namoda, jihar Zamfara

- Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun bar PDP ne saboda rashin shugabanci a jam'iyyar

- Sauyin shekar mambobin jam'iyyar na zuwa a daidai lokacin da gwamna Nyesom Wike ke cewa 'yan Nigeria sun kagu PDP ta karbi mulkin kasa a 2023

Dubban ya'yan jam'iyyar PDP a mazaɓar Kungurki cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda suka canza sheka zuwa jam'iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gungun mutanen, sun bayyana yin hijirar tasu ne a wani bikin karɓar su da aka shirya a Sabon Garin Kauran Namoda.

Da ya ke magana a madadin sauran mabiya, Malam Bala Kaura, ya ce kungiyoyi uku ne suka yanke shawarar barin jam'iyyar PDP su ka tsallaka APC sakamakon rashin shuagabancin da babu a jam'iyyar ta PDP.

"Babu wata nasara da za ka nuna sama da shekara guda da PDP ta kama mulki a wannan jihar" in ji malam Bala.

KARANTA: Wata daban: Daliban BUK sun ce basu shirya komawa ba tukunna, sun fadi dalilansu

Da take tofa albarkacin bakinta, tsohuwar shugabar matan jam'iyyar PDPn, Malama Bilkisu, ta ce sun bar jam'iyyar ne saboda halin ko-in kula na jam'iyyar.

Zugar mambobin PDP ta dunguma zuwa jam'iyyar APC a Zamfara
Zugar mambobin PDP ta dunguma zuwa jam'iyyar APC a Zamfara
Source: UGC

Ta ce tun hawan "Gwamnatin PDP ta manta da mu ba ma ganin wata nasara da ake cimmawa.

KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

"Babu wani nasara da za ka nuna sama da shekara guda da PDP ta kama mulki a wannan jihar.

"A dan haka, amadadin ɗaukacin matan jam'iyyar PDP na mazaɓar Kungurki, ina mai sanar da ficewarmu daga PDP zuwa APC" in ji malama Bilkisu.

A wani labarin na Legit.ng, Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce 'yan Nigeria sun kosa shekarar 2023 ta zo domin PDP ta koma mulkin kasa.

Gwamna Wike ya bukaci jam'iyyar APC ta yi koyi da abin da PDP ta yi a shekarar 2015 na mika mulki bayan faduwa zabe.

Wike ya gargadi jam'iyyar APC akan kar ta kuskura ta yi yunkurin sauya zabin 'yan Nigeria a shekarar 2023.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel