Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin harajin wuta

Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin harajin wuta

- Kungiyoyin masu amfani da wutan lantarki sun yi Allah wadai da karin farashin wuta a Najeriya

- Kungiyoyin sun siffanta karin da rashin adalci da saba dokar da a ka yi kan kara farashin

- Hakazalika kungiyoyin sun kalubalanci DisCOs da rashin cika ka'idar da ta dace

Kungiyoyin masu amfani da wutar lantarki sun yi fatali da karin farashin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince wa kamfanonin raba lantarki 11.

Kungiyoyin, Energy Consumer Rights and Responsibilities Initiative (ECRRI), da kuma Electricity Consumers Protection Forum, AECPF sun yi Allah wadai da ƙarin a cikin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Legas.

NERC ta amince da karin farashin wutar lantarki da zai fara aiki daga 1 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Haɗari ne gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta

Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin harajin wuta
Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin farashin wuta Credit: Naira Metrics
Asali: Facebook

”Don haka ne Hukumar ta bayyana ba tare da wani shakku ba cewa, ba a ba da izini ba kan karin farashin na kashi 50% a cikin Tsarin Farashi na kamfanonin rarraba wutar lantarki wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Janairun 2021.

”Akasin haka, farashin kwastomomi masu amfani da tsarin D & E (kwastomomin da ake ba su wuta daga awanni 12 yayi kasa) za su kasance yadda suke kuma an basu tallafi daidai da manufar tsarin Gwamnatin Tarayya.

Da yake maida jawabi, Mista Adeola Samuel-Ilori, Kodinetan kasa na AECPF, ya ce karin ya saba wa doka, rashin adalci kuma ba daidai ba ne ga masu amfani da wutar lantarki a kasar.

A cewarsa, karamin karin da ya zo bayan NERC ta kara farashin a ranar 1 ga Satumbar, 2020, ya saba da sashi na 32, 63 da 72 na dokar sake fasalin bangaren wutar lantarki (EPSRA), 2005.

Ya ce dokar ta tanadi cewa duk wani kari ya kamata a yi shi bayan tsawon watanni shida, yana mai jaddada cewa karin ya sabawa doka.

“Kamfanonin DisCos ba su cika sharadin da aka gindaya musa ba na karin kudin da a ka yi a ranar 1 ga Satumba, 2020 tun farko.

KU KARANTA: Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota

”Irin wannan yanayin ana iya samunsa a Sashe na 76 (2) (b) da (7) na EPSRA 2005 wanda ya haɗa da tattaunawa mai faɗi tare da masu ruwa da tsaki da kuma lura da ingancin aiki." in ji Mr Adeola Samuel-Ilori

A wani labarin, Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastamomi ke biya yanzu a fadin tarayya.

NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farashin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa amma unguwannin masu kudi kawai aka karawa.

Hukumar ta ce unguwannin da ke matsayin A, B, C, D da, E aka karawa farashin Kw/hr daga N2.00 zuwa N4.00.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel