Shekara da shekaru da aure, Balaraben Saudi bai taba ganin fuskar Matarsa ba

Shekara da shekaru da aure, Balaraben Saudi bai taba ganin fuskar Matarsa ba

-Shekaru da dama da su ka wuce wani Saurayi ya auri Budurwa a Saudiyya

-Yanzu aurensu ya kai shekaru 47, amma bai taba ganin fuskar matarsa ba

-Akwai mutanen da su ka yi riko da wannan al’ada da ta sabawa Musulunci

Zai yi wahala ka yarda cewa an yi shekaru 47 da yin aure, amma mai gida bai taba ganin fuskar matarsa ba, har kuma ta haifa masa ‘ya ‘ya goma.

Hakan ta tabbata, kwanakin baya wani bidiyo na wani mutumi ya bayyana, inda ya shaidawa Duniya cewa bai taba ganin fuskar uwargidarsa ba.

Jaridar Life in Saudi Arabia ta ce wannan Bawan Allah da ya yi aure ya na saurayi shekaru 47 da su ka wuce har ya zama tsoho tukuf a halin yanzu.

Duk tsawon wannan lokaci, wannan mutumi bai taba ganin ya fuskar sahibar ta sa ta ke ba.

KU KARANTA: Matarsa ta haifi yara hudu a lokaci guda, ya tsere

Da aka tambayi wannan mutum ko menene dalilinsa na haka, sai ya ke cewa shi mutumin da ne, don haka bai yarda mace ta rika bayyana fuskar ta ba.

Wannan dattijo ya ce uwargidarsa ba ta bayyanawa kowa fuskarta a Duniya, kuma haka suke zaune ko da cewa ba shi ne ya tursasa mata yin hakan ba.

Da ake hira da wannan mutum, ya tabbatar da cewa akwai wasu kabilun Larabawa a bangaren kasar Saudi Arabiya da ba su taba bari a ga fuskarsu.

Sai dai shi kan shi wannan mutum mai ‘ya ‘ya 10 ya shaidawa ‘dan jaridar cewa wannan al’ada ta su, ta sabawa addinin musulunci da ake bi a yankin.

KU KARANTA: Mai gida ya kama matarsa ta na dirkawa 'ya 'yansu giya

Shekara da shekaru da aure, Balaraben Saudi bai taba ganin fuskar Matarsa ba
Iyali a Saudiyya Hoto: BBC Daga: www.bbc.com
Asali: UGC

A cewarsa, mutane da dama sun yi fatali da wannan al’ada da ta hana mata fito da fuskokinsu, amma ya ce har gobe akwai wadanda su ka yi riko da ita.

A kasar Hausa kuma, labarin da mu ke samu shi ne wasu samari da ‘yan mata sun huro wuta, suna so a kashe lefe da kayan aure da aka saba yi a yankin.

Yaran zamanin sun bijiro da maganar iyaye su yi fatali da al'adar da aka saba yi wajen aure.

Wadannan matasa masu bibiyar shafin Twitter su na ikirarin cewa wadannan al’adu ba su da wani amfani sai jawo rayuwar karya da kokarin son a burge.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng