Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo

Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo

- Wani mahaifin yara biyar ya ci kafar kare bayan matarsa ta haifa masa karin yara hudu a lokaci daya

- Matar mai suna Rita Ndibisu ta haifi yan hudu a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu

- Wata mai amfani da shafin Facebook, Sarah Az Izevbigie, ta bayyana hakan a shafinta a ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu

Wani uban yara biyar ya tsere bayan matarsa ta haifi yara hudu zur a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu a Benin, babbar birnin jihar Edo.

Wata mai amfani da shafin Facebook mai suna Sarah Az Izevbigi ce ta bayyana hakan. A cewar matar, mai jegon mai suna Rita Ndibisu, na bukatar taimakon yan Najeriya don kula da yaranta.

Ta roki yan Najeriya da su taimaki Rita da yaranta yayinda ta wallafa asusun bankin da za a sa kudin.

Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo
Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo Hoto: Sarah Az Izevbigie
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa

Sarah ta rubuta:

“Tana bukatar taimako da tallafi daga gareni da dukkan yan Najeriya. Tsumman goyo, abincin yara, kaya kudi da duk wani abubuwan bukata domin har yanzu ba a biya kudin asibiti ba.

“Sunanta Rita Ndubisi, Lamban asusun 3147825035, First bank. Lambar wayanta 07033666031 ko kuma ayi amfani da asusuna 2007839177 Sarah iroghama Izevbigie bankin Zenith. Gudunmawarku zai taimaka sosai. Nagode kuma Allah ya biya ku.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo

A gefe guda, wani ma'aikacin kamfani, Kazeem Adebiyi, ya shaida wa wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ile-Tuntun ta raba auren sa mai shekara uku da matar sa, Rukayat bisa zargin yunkurin kashe shi da ke yawan yi da zarar sun dan samu sabani.

Da ya ke zartar da hukunci, shugaban kotun, Cif Henry Agbaje, ya raba auren, a cewar sa a samu kwanciyar hankali tsakanin Adebiyi da Rukayat.

Agbaje ya kuma mika alhakin kula da yaran su biyu a hannun Rukayat tare da umartar Adebiyi da ya dinga biyan N8,000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa, tare da daukar nauyin karatunsu da duk wata dawainiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel