Wasu ‘Yan mata da samari sun fara kiran a daina kai gara, yin akwatin lefe a aure
- Maza su kan yi wa mata akwatin lefe idan za su aure su a kasar Hausa
- Su kuma dangin matan a kan bar su ne da dawainiyar gyara gidan ango
- An samu wasu samari da ‘yan mata da su ke yin tir da wadannan al’adu
Wasu samari da ‘yan mata daga yankin Arewacin Najeriya sun fito su na sukar al’adar lefe da gara da kaya daki da aka saba yi wajen aure a zamanin nan.
Wadannan matasa masu bibiyar shafin Twitter su na ikirarin cewa wadannan al’adu ba su da wani amfani sai jawo rayuwar karya da kokarin son a burge.
Wata daga ciki masu wannan ra’ayi, Safiyyah Datti, ta ce:
“Lefe a karon kansa bai da amfani, a soke shi, mutane da-dama ba su amfani da rabin kayan akwatin. A saukaka aure kamar yadda addini ya umurta.”
KU KARANTA: Daga jego, 'yaruwata ta yi wuf da mijina
“Haka zalika a soke kayan gida da gara. A bar sabon aure su fara rayuwarsu sannu a hankali.”
Shi ma wani Bawan Allah mai suna Abdullahi UDK ya na da wannan ra’ayi, ya ce da sake. Ya ce lefe bai da wani amfani, kuma ba a bukatar shi. a aure.
“Manyan Arewa suna bukatar su zauna, su yi fatali da al’adar gayyatar mutane su zo kallon lefe. Bai jawo komai sai hassada da kuma kananan maganganu.”
Malam Abdullahi UDK ya kara da cewa ganin gidan amarya ya shiga ciki, a cewarsa babu alilin a rika shiga gida domin ganin irin kayan da aka jera a ciki.
KU KARANTA: Sadaki ya zama cika wajen aurar da 'yan mata a Kano
Amma irinsu wata Ruqayyah Hayatey sun ce abin da ya kamata shi ne kwarya ta bi kwarya wajen aure, ta haka iyaye ba za su sha wahalar aurar da yara ba.
Wasu kuma sun kare yin lefe da ake yi, su ka ce idan ba don haka ba, akwai matan da ba za su rika sanya tufafin kirki bayan sun shiga gidan mazajensu ba.
Kwanakin baya kun samu rahoto game da yadda kayan lefe ke hana aure a kasar Hausa.
Da yawa daga cikin su na kukan hada kayan lefe ke hana su yin aure a Arewacin Najeriya saboda tsabar kudi da a ke kashewa wajen hada kayan akwatin 'yan mata.
A wajen auren Hausa da Fulani, daya daga cikin batutuwan da suke tasowa wajen yin aure shine kayan lefe da namiji zai hadawa wadda ya ke neman auren na ta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng