Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa

- Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani tsohon jami'in gwamnatin jihar Nasarawa

- Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da matafiya 20 a hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Toto a da ke jihar

- Hakan ya faru ne a yau Talata, 5 ga watan Janairu kamar yadda rahoton ya nuna

Yan bindiga sun kashe tsohon sakataren ilimi na karamar hukumar Nasarawa, Malami Salihu sannan suka yi garkuwa da matafiya 20 da ke hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Lamarin ya afku ne a yau Talata, 5 ga watan Janairu da rana a hanyar mungi sharp Conner Buga Gwari, da ke yankin Gadabuke a karamar hukumar Toto.

Yan bindigan sun tsare matafiya 20 a cikin motoci uku sannan suka tisa keyarsu zuwa cikin jeji, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa Hoto: @channelstv
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo

Marigayi Salihu na cikin wadanda aka yi garkuwa da su amma sai aka tsinci gawarsa daga bisani a wani jeji da ke kusa da hanyar.

Sakataren majalisar masarautar Gadabuke, Abdullahi Baba wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce yan bindigan da yawa sun fito daga jeji sannan suka kai wa motoci hari sannan suka tisa keyar fasinjojin jeji zuwa wani waje da ba a sani ba.

“An tisa keyan tsohon sakataren ilimin wanda ke kan hanyar tafiya da abokinsa a wata mota tare da sauran mutanen amma sai aka tsinci gawarsa daga bisani a wani jeji dake kusa,” in ji shi.

Ya ce masu garkuwa da mutanen basu kira kowanne daga cikin yan uwan nasa ba.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa

A wani labarin kuma, wata Kididdigar alkaluma da jaridar TheCable ta wallafa ta nuna cewa 'yan Nigeria dubu uku da dari uku da ashirin da shidda (3,326) ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta'addanci.

Alkaluman sun nuna cewa jihohin Borno, Kaduna, Katsina, Zamafara, da Benuwe sune a sahun biyar na farko da aka fi samun asarar rayuka.

Jihohin Gombe, Kebbi, Enugu, Jigawa, da Kano sun kasance jihohi biyar mafi karacin yawan salwantar rayuka sakamakon ayyukan ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel