Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa

Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa

- Christian Madubuko, wani kwamishina a jihar Anambra, ya yi murabus daga majalisar Gwamna Obiano

- Madubuko ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu, a Akwa

- Tsohon kwamishinan ya ce ya yi murabus saboda yawan rashawa a gwamnatin Obiano

A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, kwamishinan harkokin waje, al’adu da yawan bude ido a jihar Anambra, Christian Madubuko, ya yi murabus daga matsayinsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an bayyana wasikar murabus din Madubuko mai kwanan wata 11 ga watan Disamba, 2020 ga manema labarai a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu a Akwa, babbar birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon kwamishinan ya ce gwamnatin Willie Obiano ce ta sa shi yin murabus.

Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa
Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa Hoto: @WillieMObiano
Asali: Twitter

Sai dai kuma, ya shawarci Obiano da ya tashi tsaye a kan matsalolin shugabanci sannan ya karbi ragamar kula da gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta

Kafar labaran ta bayyana cewa a shekaru uku da suka gabata, Madubuko ya yi aiki a matsayin kwamishinan masana’antu,kasuwanci, ciniki da kuma kwamishinan hanya, hanyoyin jiragen kasa da kuma sufurin ruwa.

Wasikar ta ce:

“Ina mai matukar farin ciki da nuna godiya a tsawon lokacin da muka shafe muna yi wa jiharmu hidima kuma tabbas shekaru ukun da muka shafe tare suna cike da darussa masu kyau da kuma sabanin haka.

“A fafutukar yaki da rashawa, wasu mutane da ke rike da kudaden shiga na jihar, suna ta gabatarwa da gwamnan korafe-korafe a kaina inda ake zargina da aikata munanan ayyuka daban-daban.”

Ya yi zargin cewa a lokuta da dama wasu “jakadun zalunci” sun yi kokarin bashi rashawa, inda ya kara da cewa idan mutane na yaki da rashawa, sai a dunga yi masu barazana.

Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa ya sha gwagwarmaya domin jihar ta hanyar take manyan mutane.

KU KARANTA KUMA: Bincike ya nuna yan Najeriya sun fi damuwa da rashin tsaro da talauci fiye da korona

Ya ce wadanda ya take a yanzu sune suke barazana ga rayuwarsa, inda yayi zargin cewa rayuwarsa na cikin hatsari a yanzu.

Da yake martani, kwamishinan labarai na jihar, C-Don Adinuba, ya ce gwamnatin ta amshi wasikar ajiye aikin Madubuko.

A wani labari na daban, Farfesa Khalifa Dikwa, daya daga cikin dattawa a kungiyar dattawan Borno ya nuna damuwarsa a kan hauhawar rashin tsaro a yankin.

Ya ce baya da babban birnin jihar Borno, babu inda mutane ke rayuwa da tsaro a fadin jihar.

"Ko da a ce babu Boko Haram a wasu wurare, sun riga sun tsorata jama'a kuma suna zukatan jama'a tare da hana su zaman lafiya," Dikwa ya sanar da Channels TV a wani shirin daren ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel