Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo

- Fadar Shugaban kasa ce ta tabbatar da wannan ci gaban a wani wallafa da tayi a shafin Twitter

- Ana tsammanin shugabannin biyu za su tattauna kan matakan da gwamnati ta dauka ta fuskanci tattalin arziki sakamakon annobar korona

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Janairu, ya yi ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar Shugaban kasa, Abuja.

An bayyana hakan ne a wani wallafa da fadar Shugaban kasa tayi a shafinta na Twitter. A cewar wallafar, Shugaban kasar na samun bayanai daga Osinbajo kan ci gaban da aka samu a shirin daidaita tattalin arziki zuwa yanzu.

Matakin da gwamnati ke dauka don kara kuzarin tattalin arziki a wannan yanayi na annobar korona.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawar sirri da mataimakin Shugaba Osinbajo Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa

Ganawar na zuwa ne a yayinda kasar ke gwagwarmaya da annobar korona rukuni na biyu.

A tuna cewa gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu, ta ba yan Najeriya cewa babu wani shiri na sake rufe kasar sakamakon yaki da annobar a karo na biyu.

Gwamnatin tarayya ta fayyace hakan ne ta ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Yobe da wasu jihohi 5 da suka amince da bude makarantu

A wani labarin, hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta amince da kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastomomi ke biya yanzu a fadin tarayya.

Hakan zai shafi kamfanonin raba wutan lantarki 11 dake Najeriya. Wannan na zuwa ne watanni biyu kacal da kara farashin a watan Nuwamba 2020.

A cewar umurnin waiwayan farashin shekara-shekara da sabon shugaban NERC, Engr. Sanusi Garba, ya rattaba hannu ranar 30 ga Disamba, 2020, kuma aka gani ranar Talata, an fara dabbaka sabon farashin ne fari daga ranar 1 ga Junairu, 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel