Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020

Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020

- An fuskanci matsalar tabarbarewar tsaro a cikin shekarar 2020 da ta gabata

- 'Yan bindiga, 'yan fashi da makami, masu garkuwa mutane da kuma 'yan Boko Haram sun hallaka dumbin mutane

- Kididdigar jaridar TheCable ta nuna cewa 'yan Nigeria 3,326 ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta'addanci a shekarar 2020

Wata Kididdigar alkaluma da jaridar TheCable ta wallafa ta nuna cewa 'yan Nigeria dubu uku da dari uku da ashirin da shidda (3,326) ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta'addanci.

Alkaluman sun nuna cewa jihohin Borno, Kaduna, Katsina, Zamafara, da Benuwe sune a sahun biyar na farko da aka fi samun asarar rayuka.

Jihohin Gombe, Kebbi, Enugu, Jigawa, da Kano sun kasance jihohi biyar mafi karacin yawan salwantar rayuka sakamakon ayyukan ta'addanci.

KARANTA: Hotuna: Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane

Rayukan mutane 665 aka rasa a jihar Borno sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda.

KARANTA: Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023

Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020
Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020 Hoto: Nigeria Airforce
Asali: Facebook

Alkaluman sun nuna cewa rayuka 489 sun salwantar a jihar Kaduna, 375 a jihar Katsina, 219 a jihar Zamfara, sai kuma in mutane 156 a Benuwe.

TheCable ta ce alkaluman basu hada da adadin mutanen da 'yan fashi da Jami'an tsaro suka kashe ba.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa akalla mutane tara, cikinsu har da jarirai biyu, suka rasa ransu sakamakon wani hari da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan wasu matafiya a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a daidai garin Zankoro da ke kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna.

Mukhtar Lawal, Wani mazaunin yankin da ya kawowa mutanen dauki bayan harin, ya shaidawa HumAngle cewa "tawagar 'yan bindigar sun kashe mutane da yawa cikinsu har da jarirai uku yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Biki a Doka, karamar hukumar Birnin-Gwari."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng