Gwamnan jihar Kwara ya kori Kwamishinoninsa, ya godewa aikin da su ka yi

Gwamnan jihar Kwara ya kori Kwamishinoninsa, ya godewa aikin da su ka yi

- Gwamnan Kwara ya bada sanarwar ya sallami Kwamishinonin da ya nada

- Hadimin Gwamnan ya bada sanarwa, ya ce SSG kadai ya tsallake sallamar

- AbdulRahman AbdulRazaq ya godewa mukarraban da su ka yi masa hidima

Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sauke dukkanin mukarrabansa. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto ranar Litinin.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar da jawabi ta bakin babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya na mai bada wannan sanarwar.

Kamar yadda Mista Rafiu Ajakaye ya bayyana, sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Mamman Jubril ne kadai gwamna ya bari a kan mukaminsa.

A wannan babbar kakkaba da gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi a ranar Lahadi, Mamman Jubril ne kurum wanda ya tsira da kujerarsa.

KU KARANTA: Gwamnan Kwara ya rusa gidan dangin Saraki

Ajakaye ya ce gwamna ya ba kwamishinonin da aka sauke umarnin su sallamawa manyan jami’an da ke ma’aikatunsu duk wasu aiki da ake kai.

Gwamna AbdulRazaq ya godewa duk wadanda ya yi aiki na tsawon kusan shekara daya da rabi.

Sanarwar ta ce: “Mai girma gwamna ya yi godiya ta musamman ga mukarrabansa saboda irin gudumuwar da su ka bada wajen cigaban jihar.”

Ajakaye ya cigaba da cewa: “Gwamna ya na yi masu fatan alheri a ayyukan da za su sa a gaba.”

KU KARANTA: Gwamnonin PDP a Kudu suna harin sauya-sheka zuwa APC

Gwamnan jihar Kwara ya kori Kwamishinoninsa, ya godewa aikin da su ka yi
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar ya bayyana cewa aikin kwamishinonin jihar ya kare ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

Ku na da labari cewa Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ne ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ayi maganin Coronavirus.

Mai girma gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a watan Maris, 2020.

Alhaji Abdulrahman Abdulrazak ya dauki wannan mataki ne ganin yadda attajirai suke bayar da tasu gudunmuwar domin taimakawa wajen yakar annobar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel