Wasu Gwamnonin Kudu maso gabas za su koma Jam’iyyar APC inji Ayogu Eze

Wasu Gwamnonin Kudu maso gabas za su koma Jam’iyyar APC inji Ayogu Eze

- Ayogu Eze ya ce ba da dadewa ba wasu Jihohi za su koma hannun APC

- Bayan APC ta karbe Imo da Ebonyi, jam’iyyar ta na ta harin wasu jihohin

- Eze ya ce nan ba da dadewa APC za ta kara kafa wasu gwamnoni a Kudu

Wani daga cikin manyan APC a kudancin Najeriya, Ayogu Eze, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, jam’iyyarsu za ta samu karin wasu gwamnoni.

Jaridar The Sun ta rahoto Mista Ayogu Eze ya na cewa akwai gwamnonin jam’iyyar PDP da za su fice su sauya-sheka, su dawo cikin tafiyar APC mai mulki.

Eze wanda ya tsaya a matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Enugu a jam’iyyar APC ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya raba kayan bikin sabuwar shekara.

Da ya ke rabawa ‘ya ‘yan jam’iyyar ta su ta APC wadannan kaya, an rahoto Eze ya na cewa:

KU KARANTA: Yadda za mu ci zabe - PDP

“Daminar jam’iyyar APC ta kusa kankama idan har kuwa mun iya wanke allonmu, za mu samu damar da za mu kafa sabuwar gwamnati a nan jihar Enugu.”

“Mu na bukatar mu kafa tubalin gini mai kyau, idan mu ka yi wannan, a shekarar 2023, jam’iyyar APC za ta kafa gwamnati.” Inji jagoran ‘yan hamayyar Enugu.

Eze ya ce yanzu APC ta na kara shiri, ta na hada-kai da sauran jam’iyyu domin ta yi nasara a 2023.

“Ina so kuma in fadu maku a madadin shugabanninmu ba mu sakakance ba, APC tana zama wata amarya a Kudu maso gabas, jihar Ebonyi ta fadi, Imo ta fadi.”

KU KARANTA: Jobe ya jefawa Ganduje da Shugabannin APC a Kano kalubale

Wasu Gwamnonin Kudu maso gabas za su koma Jam’iyyar APC inji Ayogu Eze
Ayogu Eze Hoto: Twitter Daga: Credit: @eze_2019
Asali: Twitter

Ayogu Eze ya ce: “Ina hasashen jiha daya ko biyu za su fadi kwanan nan.” ‘Dan siyasar ya ce idan su ka dage, akwai yiwuwar Ibo su iya fito da shugaban kasa.

Kwanan nan mu ka kawo maku rahoto game da abin da su Saradaunan Sokoto su ka hango, su ka hana a Najeriya ‘yanci a 1956, aka dakata har zuwa 1960.

Tanko Yakasai ya ce ganin an yi wa yankin Arewa nisa ya hana su yarda da ‘yancin kai kafin 1960.

Dattijon ya ce lokacin da Yarbawa su ke so a ba kasar ‘yancin-kai, kaf shiyyar Arewa mutum 1 ya shiga jami'a, ya samu shaidar Digiri, akasin sauran yankuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng