Na bada kyautar albashina na wata 10 domin yaki da Coronavirus – Gwamnan Kwara

Na bada kyautar albashina na wata 10 domin yaki da Coronavirus – Gwamnan Kwara

Gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya.

Premium Times ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi, 29 ga watan Maris, a daidai lokacin da attajiran Najeriya suke bayar da nasu gudunmuwar domin taimaka ma gwamnati wajen yaki da cutar.

KU KARANTA: Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus

A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi ba, don haka yana bukatar albashin a yanzu domin a kashe su wajen yaki da Corona, duk da cewa ba’a samu bullarta a jaharsa ba.

“Tun daga ranar 29 ga watan Mayu da aka rantsar da ni a matsayin gwamnan jahar Kwara, ban taba amsan albashi ba, amma a yanzu na kyautar da kudin duka domin a sama ma jama’anmu gajiyayyu sauki sakamakon mawuyacin halin da suka shiga bayan an hana su fita.

“Haka zalika na yi wannan ne domin na kara mana karfin yaki da cutar COVID-19 idan har ta shigo jahar Kwara, wannan lokaci ne da ake bukatar sadaukarwa daga dukkaninmu. Ina jinjina ma Minista Lai Muhammad da Gbemisola Saraki da suka sadaukar da rabin albashinsu tare da takwarorinsu don yaki da cutar.

“Bugu da kari a madadin jama’a na, ina jinjina tare da godiya ga Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu da Tony Elumelu bisa tallafin da suka baiwa jahar Kwara, da wannan ne nake kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni masu zaman kansu su yi koyi da mutanen nan ta hanyar hana hannu da jahar Kwara.

“Ana iya bayar da taimakon ga kwamitin da muka kafa, haka zalika za’a iya bayar da tallafin kayan abinci wanda zamu tabbatar da sun isa ga talakawa marasa karfi da gajiyayyu domin rangwanta musu bisa halin da suka shiga a dalilin bullar wannan cuta.” Inji shi.

Ita dai wannan sabuwar annobar Coronavirus tana toshe numfashin dan Adam ne, kuma a yanzu haka wannan cuta ta kama akalla mutane 111 a Najeriya, tare da kashe mutum 1.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel