2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbajo-Zulum tikiti

2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbajo-Zulum tikiti

- Wani jigon APC daga arewa, Abubakar Girei, ya goyi bayan kudu maso yamma ta samar da Shugaban kasar Najeriya a 2023

- Girei ya ce baiwa mataimakin Shugaban kasa Osinbajo tikiti tare da sanya gwamnan Borno ya zama abokin takararsa zai ba APC damar yin nasara a zabe na gaba

- Jigon na APC ya yi bayanin cewa rawar ganin da kudu maso yamma ta taka wajen nasarar zaben shugaba Buhari shine dalilin da yasa yake goyon bayan yankin

Abubaka Girei, wani babban jigon jam’iyyar All Progressive Congress (APC), ya bayar da shawarar baiwa Yemi Osinbajo-Babagana Zulum tikitin shugabancin kasa a 2023, cewa wannan hadin zai tabbatar da nasarar jam’iyya mai mulki.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa dan siyasan na Adamawa kuma tsohon sanata ya ce idan APC za ta mika shugaban kasarta zuwa kudu, zai fi dacewa ta baiwa mataimakin shugaban kasa mai ci tikitin domin karfafa nasarorin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Girei ya kara da cewa zabar gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takarar Osinbajo zai taimakawa jam’iyyar wajen ci gaba da kasancewa a mulki har bayan 2023.

2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbaj-Zulum tikiti
2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbaj-Zulum tikiti Hoto: Professor Yemi Osinbajo, The Governor of Borno State
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: 2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai

Legit.ng ta tattaro cewa jigon na APC ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu, a jihar Kaduna.

Tsohon sanatan ya shawarci shugabancin APC da ta guji yin gagarumin kuskure a zabenta na Shugaban kasa da abokin takararsa.

Koda dai ya ce ana kan fafutukar ganin an mika shugabanci ga kudu maso gabas, jigon na APC yayi korafin cewa tunani mai kyau shine mika shi ga kudu maso yamma saboda goyon bayan da yankin ta baiwa Buhari a zaben karshe.

Hakazalika, jigon na APC ya ce yanki mafi cancanta wajen samar da shugaban kasa a 2023 ita ce arewa maso gabas sai kudu maso gabas domin basu taba samar da Shugaban kasa a baya ba.

KU KARANTA KUMA: Tattaunawa kan Buhari ba alheri bane ga kwakwalwa ta, in ji Soyinka

Ya yi bayanin cewa dalilinsa na goyon bayan kudu maso yamma ya kasance saboda yarjejeniyar dattako da kuma rawar ganin da ta taka wajen ganin Buhari ya zama Shugaban Najeriya.

A wani labarin, tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da magabacinsa da magajinsa Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje

Shekarau, wanda a yanzu shine sanata mai wakiltar mazabar Kano Ta Tsakiya a Majalisar Tarayya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ya fadi hakan ne yayin taron manema labarai a Kano a ranar Lahadi.

Ya ce, "Ni da Ganduje mun daɗe muna tare tsawon shekaru. Lokacin da nake Sakataren dindindin a Cabinet Ofis, shi kuma kwamishina ne, kuma muna haduwa sosai."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel