Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau
- Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Jihar Kano ya ce akwai ƙyayawar alaka tsakaninsa da Kwankwaso da Ganduje
- Sanatan mai wakiltar Kano Ta Tsakiya ya ce ya san Ganduje tsawon shekaru kuma sunyi aiki tare
- Kazalika ya ce ya daɗe da sanin Kwankwaso kuma banbancin jam'iyya ba zai taɓa ɓata alaƙarsu ba
Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da magabacinsa da magajinsa Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje, The Punch ta ruwaito.
Shekarau, wanda a yanzu shine sanata mai wakiltar mazabar Kano Ta Tsakiya a Majalisar Tarayya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ya fadi hakan ne yayin taron manema labarai a Kano a ranar Lahadi.
DUBA WANNAN: Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)
Ya ce, "Ni da Ganduje mun daɗe muna tare tsawon shekaru. Lokacin da nake Sakataren dindindin a Cabinet Ofis, shi kuma kwamishina ne, kuma muna haduwa sosai.
"Ina tabbatar maka cewa tun lokacin akwai alaƙa mai kyau tsakanin mu. Don haka babu wata matsala tsakanin mu.
KU KARANTA: Allah ya yi wa ƙanin Sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota
"Haka shima Kwankwaso; akwai alaƙa ƙyayawa tsakanin mu. Banbancin mu na siyasa ba zai taɓa ɓata wannan alakar ba. Ban taɓa sauya sheka daga jam'iyya ɗaya zuwa wata saboda shi ba."
A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.
A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng