Tattaunawa kan Buhari ba alheri bane ga kwakwalwa ta, in ji Soyinka

Tattaunawa kan Buhari ba alheri bane ga kwakwalwa ta, in ji Soyinka

- Farfesa Wole Soyinka ya ce baya son yin magana kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari

- Fitaccen marubucin ya ce idan har mutum baya son ya 'zautu' ya fi alheri ya dauka babu gwamnatin

- Duk da hakan, Soyinka ya ce ya yi farin cikin ganin yadda aka gyara da gina sabbin layukan dogo da jiragen kasa

Fitaccen marubucin Najeriya da ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce idan har mutum bana son ya zautu, ya rika tsamanin kawai babu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kasar.

Amma ya bayyana layin dogo da jiragen kasa na Lagos zuwa Abeokuta a matsayin abin ban sha'awa da ya dace a yi tun da dadewa.

Tattaunawa kan Buhari zai iya taba min kwakwalwa, in ji Soyinka
Tattaunawa kan Buhari zai iya taba min kwakwalwa, in ji Soyinka. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa kanin sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota

Soyinka ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da aka yi da shi a Kaftin TV wadda wakilin The Punch ta bibiya.

Da ya ke magana a kan sabbin jiragen, fitaccen marubucin ya ce baya son ya yi magana a kan gwamnatin Muhammadu Buhari domin yana dauka ne tamkar babu gwamnatin.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojoji, sun kashe 7, sun raunata wasu

Da aka tambaye shi ko jiragen kasan sun abu ne da zai saka a yaba wa gwamnatin Buhari, ya ce, "Bana son yin magana a kan gwamnatin Muhammadu Buhari. Ina ganin ya fi zama alheri ga kwakwalwa ta baki daya. Ina iya magana kan wasu abubuwa da ke faruwa a Najeria a yanzu amma ina ganin domin kiyaye lafiyar kwakwalwar mutum, ya fi dacewa ya manta akwai gwamnatin Buhari."

Marubucin ya ce tsawon shekaru titunan Najeriya sun lalace sun zama tarkon mutuwa yayin da kasar ta yi watsi da jiragen kasa.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel