Buhari da jerin fitattun ‘Yan siyasan da za a zurawa idanu a shekarar bana

Buhari da jerin fitattun ‘Yan siyasan da za a zurawa idanu a shekarar bana

- ‘Yan siyasar Najeriya sun soma yin tanadi domin 2023 tun a halin yanzu

- Akwai wasu ‘Yan siyasa da ake yi wa ganin su na hangen zabe mai zuwa

- Daga ciki akwai irinsu Bola Tinubu, Dr. Kayode Fayemi da Nyesom Wike

’Yan siyasan Najeriya su na da dogon hange, kuma wannan shekara za ta fi ta bara ganin kintsi da shirye-shiryen manyan ‘yan siyasar kasar nan.

Legit.ng ta kawo maku jerin wasu ‘yan siyasa da ake ganin cewa su za su cika labarai a bana:

1. Bola Tinubu

Na farko a jerin na mu shi ne jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu wanda ake tunanin cewa babu abin da ya ke hange sai kujerar shugaban kasa a 2023.

2. Kayode Fayemi

Masu hasashe da fashin bakin siyasa su na ganin cewa gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi tarayya da tsohon mai gidansa wajen neman takarar nan.

3. Orji Uzor Kalu

Tsohon gwamnan Abia Orji Kalu ya na cikin manyan ‘yan siyasar kasar Ibo. Sanata Kalu wanda ya fito daga gidan yari a 2020 ya na dogon buri a jam’iyyar APC

4. Dave Umahi

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya na cikin manyan wadanda ya kamata a sa wa ido a bana, musamman bayan ganin ya yi watsi da PDP, ya koma tafiyar APC.

KU KARANTA: Bola Tinubu bai da lafiya har ta kai an kwantar da shi a gadon asibiti

5. Nyesom Wike

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya na daga cikin kusoshin jam’iyyar hamayya da ya dace mutane su rika kallon inda su ka sa gaba a shekarar 2021.

6. Babagana Zulum

Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya shiga sahun manyan ‘yan siyasar da ake bibiya a Najeriya tun bayan da ya karbi mulki daga hannun Kashim Shettima.

7. Nasir El-Rufai

Wasu na tunanin gwamna Nasir El-Rufai zai nemi kujerar shugaban kasa a 2023, tsohon Ministan ya nuna ba abin da yake gabansa ba kenan, a zura masa idanu.

8. Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi ya na cikin ‘yan gaban goshin shugaba Muhammadu Buhari, kuma wanda su ka dade a kujerar Minista, da alamu tsohon gwamnan ya na da wani shiri.

KU KARANTA: Shugaban PDP ya tattara mutane sun koma APC

Buhari da jerin fitattun ‘Yan siyasan da za a zurawa idanu a shekarar bana
Taron majalisar kolin APC Hoto: BBC, www.bbc.com/pidgin/tori-53180988
Source: UGC

9. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya na cikin gogaggun ‘yan siyasa a Afrika. Bayan ya sha kashi a 2019, alamu na nuna har yanzu bai yi sanyi ba.

10. Muhammadu Buhari

Duk da ya gama neman takara, ba za a cire Mai girma Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo a matsayinsu na shugaban kasa da mataimakinsa daga cikin lissafi ba.

Kwanakin baya mun kawo maku labarin rikicin cikin gidan APC a jihar Imo inda wani hadimin Sanatan APC ya ragargaji kan Gwamna Hope Uzodinma.

Hadimin na Rochas Okorocha ya ce za su koyawa Gwamna Uzodinma darasi a APC kwanan nan.

Har yanzu ana fama da sabon rikici a APC duk da jam’iyyar ta karbe mulki daga hannun PDP a Jihar Imo a sakamakon wani hukuncin da kotun koli ta yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel