Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC

Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC

- Danlami Yanga, shugaban jam'iyyar PDP a gundumar Gwargwada da ke Toto jihar Nasarawa ya koma APC

- Ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC tare da magoya bayansa a wani taron masu ruwa da tsaki a Gadabuke

- Ya tabbatar da cewa salon mulkin gwamna Abdullahi Sule ne ya ja shi da mabiyansa zuwa jam'iyyar APC

Shugaban jam'iyyar APC na gundumar Gwargwada da ke karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa tare da daukacin mabiyansa sun koma jam'iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar, Danlami Yanga tare da mabiyansa sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a garin Gadabuke.

Ya ce: "Ni da mabiyana mun yanke hukuncin barin PDP tare da komawa jam'iyyar APC sakamakon salon mulkin Gwamna Abdullahi Sule da kuma kakakin majalisar jiha, Balarabe Abdullahi.

KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

Shugaban PDP da daukacin mabiyansa na jihar baki daya sun sauya sheka zuwa APC
Shugaban PDP da daukacin mabiyansa na jihar baki daya sun sauya sheka zuwa APC. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Ina kira ga magoya bayana da mutanen yankina da su bai wa wannan mulkin duk goyon bayan da ya kamata," yace.

Idan za mu tuna, tsohon dan majalisa a yankin, Madaki Ada-Goje tare da wani tsohon ma'aikaci a hukumar habaka yankin Gadabuke, Benjamin Belodu sun bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas

A wani labari na daban, 'yan sandan Najeriya sun sake damke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a kan jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.

Sowore tare da wasu 'yan gwagwarmaya sun shiga hannun 'yan sandan bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, zanga-zangar da suka shirya a dukkan fadin kasar nan ana gobe sabuwar shekara.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka arce ne suka tabbatarwa da Premium Times cewa an damke Sowore inda aka jefa shi daya daga cikin motocin 'yan sanda bakwai da aka tura wurin zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng