Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha

Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha

- Sam Onwuemeodo ya fadi abin da ya hana Rochas Okorocha zuwa taron Imo

- Hadimin na Rochas Okorocha ya yi kaca-kaca da Gwamnatin Hope Uzodinma

- Onwuemeodo ya ce duk wasu kusoshi da APC ta ke ji da su sun gujewa taron

Hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Sam Onwuemeodo, ya bayyana abin da ya hana mai gidansa Rochas Okorocha, zuwa wani taro na APC da aka yi.

Kwanan nan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun hadu sun yi wani taro a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri.

Sam Onwuemeodo ya yi bayanin abin da ya sa Rochas Okorocha bai samu halartar wannan taro ba.

Da yake hira da ‘yan jarida a ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020, Sam Onwuemeodo ya zargi gwamna Hope Uzodinma da kashewa APC kasuwa.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya bayyana dabarar da PDP za ta yi domin lashe zabe

Onwuemeodo ya kira wannan taro da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin kasa su ka gudanar a karkashin jagorancin Hope Uzodinma a matsayin shiririta.

Da aka tambayi hadimin Sanatan, sai ya ce: “Mutane nawa ku ka gani a wajen wannan taron? ‘Yan majalisar wakilan tarayyar Najeriy nawa su ka je?

Ya ce: “Kun ga Sanata Rochas Okorocha, Sanata Ifeanyi Ararume, ko Sanata Orji Uzor Kalu da duk manyan shugabannin jam’iyya a wajen wannan taron?

“Kusan shekara guda kenan tun da Hope Uzodinma ya zama gwamna, kuma bai taba kiran wani taron APC a Imo ba. Taron, shirmen ‘yan siyasa ne kawai”

KU KARANTA: Jerin wasu fitattun mata 10 a Najeriya da su ka fi kowa tashe a 2020

Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha
Tsohon Gwamna Rochas Okorocha Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar Onwuemeodo, nan gaba kadan za a banbamce tsakanin zare da abawa a siyasar jihar Imo.

“Duk wadanda su ka kai APC kudu maso gabas ba su wurin taron. Mu na kalubalantar su kawo sakamakon zaben akwatinsu na 2015 da 2019.” Inji Onwuemeodo.

A jiya mun tattaro maku wasu manyan al'amuran siyasa da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

Daga ciki har da sauke Adams Oshiomhole daga shugabancin APC da rikicinsa da Godwin Obaseki da kuma sake naɗa shugaban hukumar zabe da aka yi

Haka zalika mun kawo maganar rikicin Bala Muhammad da Yakubu Dogara a Bauchi da kuma sauyin-shekar wasu 'yan siyasa irinsu Sanata Elisha Abbo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel