Gwamnatin Tarayya tayi amai ta lashe, ta dawo da rajistar SIM da ta dakatar
- Wani sabon umarni ya fito daga gwamnatin tarayya kan rajistar layin wayoyi
- Hukumar NCC ta ce ta janye dakatarwar da ta yi a kan rajistar SIM kwanaki
- ALTON ta ji tausayin wadanda su ka gaza rajista ko gyara layukan wayoyinsu
Yanzu nan mu ke ji daga This Day cewa hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa ta dauki sabon mataki game da rajistar layin wayoyi.
Gwamnatin tarayya ta bada sanarwa cewa an dakatar da maganar daina yin rajistar sababbin layi da tusa rajistar tsofaffin layukan wayoyi a Najeriya.
Legit.ng ta fahimci wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban jami’in hulda da jama’a na hukumar NCC ta kasa, Mista Ikechukwu Adinde.
Ikechukwu Adinde ya fitar da jawabi a ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020 a madadin NCC.
KU KARANTA: ATOASDA ta nemi Gwamnati ta janye dokar hana rajistar layin waya
Adinde ya bayyana cewa akwai sharadi kafin ayi wa mutum rajistar layin wayarsa, dole kuwa ya zama mutum ya na da lambar NIN ta zama ‘dan kasa.
Darektan yada labaran ya ce NCC ta dauki wannan mataki ne domin karasa cin moriyar nasarorin da gwamnati ta samu wajen rajistan layin waya.
Wannan ita ce sanarwar karshe da ta fito daga bakin hukumar NCC a shekarar 2020, yayin da ake bikin murnar shiga sabuwar shekara a Najeriya da Duniya.
Kungiyar ALTON ta masu rajistar layin waya ta ji tausayin wadanda su ka shiga matsi a sanadiyyar wannan mataki da gwamnati ta dauka a da.
KU KARANTA: NCC ta shigo da tsarin dawowa mutane da ragowar 'Data' da ya yi kwantai
A dalilin haka an hana rajistar duk wani sabon layi, sannan masu neman tasa rajistarsu ba su samu damar yi ba, hakan ya toshewa wasu hanyar samu.
A shafinta na Twitter, hukumar NCC ta cigaba da yin kira ga mutane su yi rajistar lambar NIN. Wannan ya zo ne a sakon barka da shiga sabuwar shekara.
A gefe guda kuma kun ji cewa za a iya rufe layin wayoyin mutane kusan miliyan 162 saboda rajistar NIN da Gwamnatin tarayya ta wajabtawa jama'a.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce dole a hada kowane layi da lambar NIN din mai ita.
Amma masu nazari su na ganin cewa zai yi wahala a iya yi wa miliyoyin mutanen da ake da su a Najeriya wannan aiki a cikin 'yan kwanakin da aka bada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng