Lanre Sanusi ya kammala MBA da maki 3.8 a cikin 4.0 a Jami’ar Dallas

Lanre Sanusi ya kammala MBA da maki 3.8 a cikin 4.0 a Jami’ar Dallas

- Lanre Sanusi ya kammala Digirinsa na MBA a Jami’ar Dallas Baptist

- Sanusi shi ne ‘Dan Najeriyan farko da ya yi karatu a Jami’ar tun 2015

- Wannan Bawan Allah ya samu maki 3.8 a matsayin CGPA din karshe

Wani dalibin Najeriya, Lanre Sanusi ya karya tarihin shekaru biyar da aka kafa a jami’ar Dallas Baptist da ke garin Texas, kasar Amurka.

Lanre Sanusi ya zama abin bugawa a jarida ne bayan ya kammala digirinsa na MBA a jami’ar.

Abin sha’awar shi ne, Mista Lanre Sanusi shi ne ‘dan Najeriya na farko da ya iya yin karatu a wannan babbar jami’ar cikin shekaru biyar.

Wannan mutumi ya samu shaidar digirgir a fannin kasuwanci, kuma ya kammala karatun ne bayan samun nasarar 95% a kwas din da ya yi.

KU KARANTA: Talauci ya fi COVID-19 masifa - Falana

The Nation ta ce a cikin maki 4.0 da aka ware na CGPA ga daliban digiri a jami’o’in kasar Amurka, Sanusi ya kammala karatunsa ne da maki 3.8.

Sanusi ya na cikin zakakuran daliban da makarantar ta yaye a wannan shekara. Shekaru fiye da 120 da su ka wuce aka kafa wannan jami’ar.

Kafin yanzu, Sanusi ya yi karatu a Tarrant County College da jami’ar Texas (duk a nan Amurka) inda ya samu shaidar Digiri a bangaren kimiyya.

Bugu da kari, Lanre Sanusi ya na karatun digirinsa na uku watau PhD a ilmin shari’a, yanzu haka a wata jami’ar da ake kira Northeast University.

KU KARANTA: Sanusi II bai samu halartar makoki ba, ya yi wa Mahaifin Kwankwaso addu’a

Lanre Sanusi ya kammala MBA da maki 3.8 a cikin 4.0 a Jami’ar Dallas
Prince Lanre Sanusi Hoto: www.theimpactnewspaper.com
Asali: UGC

Ainihinsa mutumin Ijede ne a garin Ikorodu, jihar Legas. Wannan masani ya saba taimakon marasa karfi a Najeriya domin su yi kasuwanci.

A yau ne kuma mu ka samu labari cewa kungiyar AfBA za ta ba tsohon Shugaban kasar Najeriya Dr. Goodluck Jonathan lambar yabo a kasar Nijar.

Sannan AfBA ta ce ta gama magana da wasu tsofaffin shugabanni (har da Goodluck Jonathan) da za su yi magana a wajen babban taron ta na 2021.

Kungiyar lauyoyin ta Afrika ta na ganin Goodluck Jonathan ya na taka rawar gani a Nahiyar

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel