Jiragen Operation Lafiya Dole sun yi wa ‘Yan Boko Haram barin wuta a Sambisa

Jiragen Operation Lafiya Dole sun yi wa ‘Yan Boko Haram barin wuta a Sambisa

-Dakarun Sojojin Najeriya sun kai wani hari cikin tsakiyar dajin Sambisa

-An hallaka ‘Yan Boko Haram da su ke barna a Adamawa da Borno a harin

-Sojojin saman kasar sun yi nasarar raga-raga da mafakar ‘Yan ta’addan

‘Yan ta’addan da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da su ke kai hari a jihohin Borno da Adamawa sun gamu da karshensu a dajin Sambisa.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, cewa an hallaka wasu daga cikin mayakan ‘yan ta’addan a yankin Sambisa.

Sojojin sama da ke cikin dakarun of Operation Lafiya Dole ne su ka shiga dajin da wasu jiragen sama na yaki, su ka laluba, su ka kashe ‘yan ta’addan.

Rahotanni sun bayyana cewa ana tunanin an kashe wadanda su ke kai hari a yankunan Borno da Adamawa da ke fake a cikin wannan kungurmin daji.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kashe Miyagu a Jihar Katsina

Wani babban jami’in tsaro na kasar, Manjo Janar John Enenche, ya fitar da jawabi game da harin.

“Sojojin sama da ke cikin dakarun Operation LAFIYA DOLE su na cigaba da lallasa ‘yan ta’addan Arewa maso gabashin Najeriya.” Inji Janar Enenche.

Jami’in ya ke cewa: “Harin da aka yi a karshe shi ne wanda aka yi nasarar kai wa ranar 28 ga watan Disamba, 2020 a kirjin dajin Sambisa, Borno."

John Enenche ya ce sun kai farkami a jere, wanda hakan ya sa aka yi dacen ruguza inda ‘yan ta’addan su ke fakewa da wuraren adana kayan yaki.

Jiragen Operation Lafiya Dole sun yi wa ‘Yan Boko Haram barin wuta Sambisa
John Enenche ya na jawabi Hoto: Twitter/ @defenceinfong
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun ji haza a hannun Sojoji a Kaduna

Jawabin sojan kasa ya ce mayakan na Boko Haram sun yi yunkurin harbin jiragen sojojin amma ba su yi dace ba, a karshe an lallasa wasu daga cikinsu.

A lokacin da ake bikin kirsimeti, idan za ku tuna, 'yan ta'addan da ake zargin 'yan Boko Haram ne, sun kai hari a wasu kauyukan Borno da na Adamawa.

Sanatan Borno, Alu Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren da kungiyar Boko Haram su ke yi.

Sojojin Boko Haram sun batar da kama, sun aukawa kauyen Pemi da ke jihar Borno da garin Garkida da ke karamar hukumar Gumbi a jihar Adamawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel