Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe shugabanni 2 a jihar Kaduna

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe shugabanni 2 a jihar Kaduna

- Kungiyoyin yan ta’adda a yankin arewa maso yamma na ci gaba da yin barna a garuruwa

- Musamman jihar Kaduna, na ci gaba da fuskantar hare-haren yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci daban-daban

- Kisan baya-bayan nan da aka yi shine na wasu shugabanni biyu wadanda kungiyoyin ta’adda suka halaka a jihar Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun kai hari kauyen Kawan Rafi da ke karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna sannan suka kashe Danleeman sah, babban limamin kauyen.

A cewar rahoton, yan bindigan sun kai farmaki gidan marigayin inda suka harbe shi, sannan suka bar shi a wajen ba tare da sun dauki komai ko satar wasu mutanen ba.

KU KARANTA KUMA: Wata mai tsohon ciki ta bayyana yadda ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe shugabanni 2 a jihar Kaduna
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe shugabanni 2 a jihar Kaduna Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

An tattaro cewa an alakanta kisan mlamin da da’awarsa ta bayyana tsagwaran adawa a kan yadda ’yan bindiga ke kashewa da garkuwa da mutane a yankin.

Hakazalika, wasu masu garkuwa da mutane sun kashe Sarkin Yakin a Godogodo, Mista Yohanna Abu.

KU KARANTA KUMA: Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kisan jagororin biyu a cikin wata sanarwa.

Moses Baba ya rubuta a shafin Facebook:

“Ku kare kanku, Najeriya tamkar iyalai ne da ba su da iyalai. Ku kare kanku.”

Hashim Nyabali ya rubuta:

“Wadannan mutanen Boko Haram ne, babu wasu yan bindiga.”

Emmanuel Nwanneh ya rubuta:

“Idan kayi magana game da hauhawan rashin tsaro a kasar nan, wasu yan kashenin Buhari za su kare shi sosai. Wannan ya zarce siyasa, addini ko kabilanci.”

A wani labarin, jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun dakile harin da yan bindiga suka kai wani gari dake wajen karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

A cewar kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce wannan abu ya auku ne misalin karfe 4:30 na daren Asabar, ChannelTV ta ruwaito.

SP Shehu ya ce hukumar ta samu labarin cewa yan bindiga sun dira wajen Shinkafi da niyyar garkuwa da mutanen garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel