Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa

Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa

- Wani dan rikon Iyan Zazzau ya karyata jita-jitar da ake yadawa ta cewa kashe marigayin aka yi

- Yaron wanda ya kasance Tafidan Dawakin Zazzau ya ce jita-jitar da ake yadawa ta kisan mahaifin nasa ba ta da wani asali ballanta tushe

- A yau Asabar, 2 ga watan Janairu ne aka binne marigayin a Sabon Gari

Dan rikon marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo na cewa kashe marigayi yariman Zazzau wanda ke shari’a da gwamnatin jihar Kaduna kan zabar sarkin Zazzau na 19 aka yi.

Legit.ng ta samu labarin rasuwar Aminu a jihar Lagas a safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu.

An dauki gawarsa zuwa Sabon Gari, jihar Kaduna, a ranar Asabar inda aka yi sallar jana’izarsa a masallacin Juma’ar da ke yankin kafin aka binne shi a gidansa.

Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa
Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa Hoto daga Haleema Khalid
Source: Facebook

Jim kadan bayan sanar da labarin mutuwarsa a Kaduna a ranar Juma’a, sai jita jita ya fara yawo a jihar cewa an kashe marigayi yariman a Lagas lokacin da fito daga gidansa don zuwa mallaci don sallar Asubahi a ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Galadima ya bayyana wadanda suka kulla yarjejeniyar mulkin karba-karba a APC

Sai dai da yake zantawa da jaridar Daily Trust bayan binne marigayin, Shehu Iya Sa’idu wanda ke rike da mukamin Tafidan Dawakin Zazzau kuma dan marigayi Iyan Zazzau ya ce jita jitan kisan bai da tushe.

Ya kara da cewa kasancewarsa daya daga cikin makusantan marigayin, yana iya tabbatar da cewa mutuwar Allah marigayin yayi.

“Ya yi fama da rashin lafiya, amma saboda shi mutum ne mai jarumta, mutane da dama basu san da hakan ba face mu da muke kusa da shi,” in ji shi.

“Jita jitan harbi ba gaskiya bane kuma ina daya daga cikin makusantanshi saboda mahaifina ne ya rike shi sannan shima ya rike ni tun ina shekaru biyu.

“Don haka ina iya fada maku cewa lokacinsa ne yayi kuma Allah Ubangiji wanda ya bamu shi ya karbi abinsa.

“Addu’anmu shine Allah ya yi masa rahama sannan ya bashi Alhannah Firdausi,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria

Sa’idu ya ce an dawo da mahaifin nasa gida domin a binne shi saboda ya bar wasiyyan cewa a yi masa jana’iza a masallacin Juma’a na Sabon Gari.

“Muna yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya bamu ikon sauke wannan nauyi na wasiyya da bayar," in ji shi.

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki a kan mutuwar manyan jagorori biyu a Masarautar Zazzau, Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da Talban Zazzau, Abubakar Pate a rana daya.

A sakon ta’aziyya da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya saki a ranar Juma’a a Abuja, Buhari ya bayyana mutuwarsu a matsayin abun bakin ciki biyu.

Shehu ya ce Shugaban kasar ya tura tawaga zuwa Fadar Sarkin Zazzau don gabatar da ta’aziyya a madadinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel