Wata mai tsohon ciki ta bayyana yadda ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane
- Washegarin ranar bikin Kirsimeti, an yi garkuwa da wata yar shekara 22 mai tsohon ciki daga kauyenta a Katsina
- Da take bayyana halin da ta shiga, Suwaiba Naziru ta ce sun yi tattaki na tsawon kilomita sannan suka tsere kan babura zuwa mafakarsu
- Suwaiba ta haifi diya mace yayinda take a hannun wadanda suka sace ta wadanda suka sama mata dukkan abunda take bukata na haihuwa
Yan bindiga a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba, 2020, da misalin karfe 8:00pm sun kai hari Biya Ki Kwana da ke karamar hukumar Batsari, jihar Kaduna.
Yan bindiga sun yi garkuwa da Suwaiba Naziru, wacce ke da haihuwa daya da kuma tsohon ciki tare yar tata mai shekaru biyu.
Har ila yau an sace mata 10 da yara biyu yayinda aka harbi wasu matasa biyu.
A wata hira da jaridar Daily Trust, Suwaiba ta yi bayanin abunda ya faru da ita a wannan dare da yadda ta haifi diya mace a dajin yayinda masu garkuwa da mutanen ke kallo.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Galadima ya bayyana wadanda suka kulla yarjejeniyar mulkin karba-karba a APC
Ta ce a wannan rana ta fita domin kiran mijinta a waya domin fada masa cewa ya turo kudi gida don su siyi kayan abinci.
A hanyarta, sai ta hadu da yan bindiga tare da wasu matan da suka riga suka sace.
Ta bayyana cewa:
“Sun bukaci na tafi tare da su amma na fada masu cewa Ina da tsohon ciki. Sai suka ce karya nake yi, don haka suka tilasta ni shiga sahun sauran matan sannan aka ingizamu zuwa jeji kamar garken shanu.
“Kamar yadda na fadi, na sanar masu, amma suka ce karya nake yi har sai da na fara nakuda sannan suka gane cewa gaskiya ne.”
Suwaiba ta ce tafiyar ta kasance mai tsananin wahala domin bayan tsohon ciki, tana dauke da goyo a hannunta yayinda suka yi dogon tafiya.
A cewarta, lokacin da ta fara nakuda, sai daya daga cikin sauran matan ta zama unguwar zoma. Masu garkuwan sun samar da reza don yanke cibi da ruwan zafi don wankan mejego da jinjirar.
KU KARANTA KUMA: Ba kashe Iyan Zazzau aka yi ba, mutuwar Allah yayi, dansa
Suwaiba ta bayyana cewa suna da bukka inda suke zama ba tare da tabarma, don haka a kasa suke kwanciya.
Ta ce sauran matan na nan a hannun masu garkuwa da mutanen inda suka nemi ta fada ma mazauna kauyen cewa koda zai zamana za su yi roko don tara wasu kudade don ceto, toh kada su yi kasa a gwiwa don ceto su daga wadanda suka sace su.
A wani labari, Jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun dakile harin da yan bindiga suka kai wani gari dake wajen karamar hukumar Shinkafi ta jihar.
A cewar kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce wannan abu ya auku ne misalin karfe 4:30 na daren Asabar, ChannelTV ta ruwaito.
SP Shehu ya ce hukumar ta samu labarin cewa yan bindiga sun dira wajen Shinkafi da niyyar garkuwa da mutanen garin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng