Shugaban kasa 2023: Galadima ya bayyana wadanda suka kulla yarjejeniyar mulkin karba-karba a APC
- Ana muhawara a APC game da ko har yanzu akwai batun yarjejeniyar mulkin karba-karba
- Alhaji Buba Galadima ya tabbatar da cewar akwai yarjejeniyar mulkin karba-karba a tsakanin wasu jiga-jigan APC
- Galadima, tsohon na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci shugabannin APC da su riki yarjejeniyar
Shugaban sabuwar jam’iyyar Reformed All Progressives Congress, R-APC, Alhaji Buba Galadima ya kaddamar da cewar a yayin kafa jam’iyyar, akwai yarjejeniyar mulkin karba-karba da shugabannin jam’iyyar mai mulki suka yarda da shi.
Galadima ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Sun wanda aka wallafa a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu.
Sai dai, ya bayyana cewa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin APC, babu wata kalma na mulkin karba-karba a cikinta.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya kadu matuka da rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau
Kalamansa:
“Na ji daga majiya abun dogaro cewa akwai yarjejeniyar dattak a tsakanin wasu jiga-jigai daga kudu maso yamma da arewa cewa idan kudu maso yamma suka mara masu baya Buhari ya lashe zaben 2015 cewa arewa za ta marawa dan takarar kudu maso yamma baya a 2023.
“Wannan yarjejeniyar dattako ne. Bari na kuma ce alkawari, alkawari ne, kuma idan kayi alkawari ya zama dole ka cika wannan alkawarin.
“Wadanda suka zauna sannan suka amince da wannan yarjejeniyar sune tsoffin gwamnoni biyu daga kudu maso yamma, gwamna mai ci daga arewa, da kuma wani jigon siyasa daga arewa, sune suka sanya hannu a wannan yarjejeniyar. Ya kasance muhimmin yarjejeniya.”
Da aka tambaye shi ko yana cikin yarjejeniyar, ko ya taka wani rawar gani a yarjejeniyar, Galadima ya ce:
“Ba na cikin yarjejeniyar amma wadanda ke cikin yarjejeniyar da suka kulla sun fada mun. Idan mutanen APC na da mutunci, dole ne su cika alkawarinsu. Idan shugabannin jam’iyyar na da gaskiya, dole ne su aiwatar da wannan yarjejeniyar.”
KU KARANTA KUMA: Sakon sabuwar shekara: Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su rungumi adalci da zaman lafiya
A wani labarin, wani fasto mazaunin kasar Ghana, Prophet Nigel Gaisie, ya yi hasashen cewa mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai zama Shugaban kasar Najeriya.
BBC ta ruwaito cewa faston, wanda ya kasance Shugaban cocin Prophetic Hill Chapel Prophet ya yi hasashen a lokacin wa’azinsa na shiga 2021.
Sai dai Gaisie, bai yi bayani kai tsaye ba kan ko hasashensa kan Osinbajo zai zo ne bayan gwamnatin Buhari ko kuma wani lokaci a nan gaba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng