Shahararrun matan da su ka fi kowane yawan shiga cikin labarai a shekarar nan
Yayin da ake ban-kwana da shekarar 2020, a shiga 2021, jaridar Daily Trust ta tattaro jerin wasu mata da su ka fi kowa yawan fitowa a labarai.
A wannan shekara da za a fita, wadannan mata sun kasance abin labari saboda irin gwawarmaya, siyasa, sana’a, ko aikin da aka sansu da shi.
Ga wadannan mata nan kamar haka:
1. Tolulope Arotile
Marigayiya Tolulope Arotile ta zo ta farko a jerin bayan irin fice da ta yi wajen tukin jirgin saman yaki. Tolulope Arotile wanda sojar sama ce ta mutu ne sanadiyyaregty hbun hadarin mota a Kaduna.
2. Rahama Sadau
‘Yar wasar Kannywood, Rahama Saudau, ba bakuwar shiga wannan jeri ba ce. Tauraruwarta ta cigaba da haskawa a bana, ta jawo surutai saboda irin hotunan da ta ke wallafawa.
3. Aisha Yesufu
Wata mata da sunan ta ya kara shiga gari a wannan shekara ta 2020 ita ce Aisha Yesufu. Wannan Baiwar Allah da aka sani da BringBackOurGirls ta kara yin suna #EndSARS.
KU KARANTA: Kwankwaso su na zaman makoki, Sarkin Kano ya je ya yi gaisuwa
4. Aisha Buhari
Ba yau aka fara tsintar mai dakin shugaban kasa a wannan rukuni ba. Aisha Buhari ta jawo abin magana wannan shekarar dalilin takkadamar ta da wasu hadiman Mai gidanta.
5. Sadiya Umar Farouq
Ministar bada agaji da tallafin gaggawa Sadiya Umar Farouq, ta samu karin shahara a shekarar nan, musamman bayan ta auri hafsun sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar.
6. Ngozi Okonji-Iweala
Tsohuwar Ministar Najeriya Ngozi Okonji-Iweala ta na cikin wannan jeri. Dr. Okonji-Iweala ta zama abin labari ne bayan ta shiga takarar WTO, kuma ta na daf da samun nasara.
7. Fatima Ribadu
‘Diyar Nuhu Ribadu, Fatima Ribadu, ta zama abin labari a karon farko a 2020, hakan ya faru ne bayan hotunan aurenta sun bayyana, inda aka zarge ta da yin shiga maras kyau.
8. Maryam Booth
Tauraruwa Maryam Booth ta masana’antar Kannywood ta shiga bakin mutane a bana bayan wani bidiyon da ake zargin ita ce a wani irin yanayi ya bayyana a shafin yanar gizo.
KU KARANTA: Irin nasarorin da mu ka yi a shekarar nan - EFCC
9. Hanan Buhari
‘Diyar shugabar kasa Hanan Buhari ta samu shiga wannan sahu tun daga lokacin da ta hau jirgin shugaban kasa zuwa wani biki, a shekarar nan ne kuma ta auri Turad Sha’aban.
10. Maryam Sanda
Har yanzu ba a bar labarin Maryam Sanda ba, wannan mata ta sake shiga kanun labarai kwanaki bayan kotu ta tabbatar mata da hukuncin kisa a sakamakon kashe mijinta da ta yi.
Dazu kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin tiriliyan 13.588. Ana sa ran wannan ne kudin da Najeriya za ta kashe a shekarar 2021.
Wadanda suka halarci taron sa hannu a kan kasafin kudin sune; Yemi Osinbajo, Ahmad Lawan, Femi Gbajabiamila da wasu manyan 'yan majaisar dattawa da na wakilai na tarayya.
A yau Alhamis ne ranar karshe a shekarar 2020.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng