Rasuwar Mahaifi: Aminu Ado Bayero ya ziyarci tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso

Rasuwar Mahaifi: Aminu Ado Bayero ya ziyarci tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso

- Aminu Ado Bayero ya yi wa Rabiu Kwankwaso ta’aziyyar rashin da aka yi masu

-Mahaifin tsohon Gwamnan, Hakimin Madobi, Alhaji Musa Kwankwaso ya rasu

-A makon nan aka yi sadakar uku na mutuwar Majidadin Kano (Makaman Karaye)

Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya taka zuwa gidan tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa ta’aziyya.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya rasa mahaifinsa watau Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, wanda ya kasance Hakimin garin Madobi.

Alhaji Aminu Ado Bayero da tawagarsa sun yi wa tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ta’aziyyar wannan babban rashi da ya same su.

Kwankwaso da sauran ‘yanuwa da abokan arziki sun karbi gaisuwar ne a gidan tsohon gwamnan da ke titin Miller, a Bompai, jihar Kano.

KU KARANTA: Buhari ya aikawa Kwankwaso ta'aziyya

Wadanda su ka tarbi Mai martaban sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf, Ahmad Abdussalam Gwarzo, da sauransu.

Bayan addu’o’i a dakin karbar gaisuwa inda ake makoki, Mai martaba da sauran jama’a sun je inda aka birne Marigayin, sun yi addu’a.

Hadimin tsohon Ministan tsaron Najeriyar, Malam Saifullahi Hassan ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar 29 a watan Disamba, 2020.

Kafin yanzu manyan jami’an gwamnatin jihar Kano, Ministocin gwamnatin tarayya, tsofaffin gwamnoni da ‘yan majalisa sun zo ta’aziyya.

KU KARANTA: Ina neman shawarar manya inji Aminu Ado-Bayero

Rasuwar Mahaifi: Aminu Ado Bayero ya ziyarci tsohon Gwama Rabiu Kwankwaso
Aminu Ado Bayero da Kwankwaso Hoto: Twitter @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Musa Saleh Kwankwaso ya rasu ne a gidansa a ranar Juma’a, ya na mai shekaru 93 a Duniya.

Idan za ku tuna, Musa Saleh Kwankwaso ya na cikin Hakiman da su ka fi dadewa a mulki a Kano, ya na kan kujera Ado Bayero ya zama Sarki.

Sabo Nanono, Hadi Sirika, Nasiru Gawuna, Ahmad Makarfi, Kabir Marafa, Bala Mohammed da wasunsu sun yi wa 'Dan siyasar gaisuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel