Gwamnatin Jahar Gombe Ta Biya Diyyar Filaye Zunzurutun Kudi N873M

Gwamnatin Jahar Gombe Ta Biya Diyyar Filaye Zunzurutun Kudi N873M

- Gwamanatin jahar Gombe ta bayyana biyan diyyar filaye da gidaje a jahar

- Gwamnatin ta bayyana rusa gidajen a matsayin aikin cigaban jahar

- Kimanin N873 ne gwamnatin ta rabawa wadanda abin ya shafa

KU KARANTA: Na yanke kauna da gwamnatin Buhari, In ji kakakin kungiyar Arewa

Gwamnatin jihar Gombe a ranar Laraba ta bayyana cewa an biya N873m a matsayin diyya ga masu filaye a jihar, Punch ta ruwaito.

Gwamnatin Jahar Gombe Ta Biya Diyyar Filaye Zunzurutun Kudi N873M
Gwamnatin Jahar Gombe Ta Biya Diyyar Filaye Zunzurutun Kudi N873M Hoto: Facebook/Premium Times
Asali: Facebook

Da yake bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron zartarwar jihar wanda Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, kwamishinan yada labarai, Alhassan Ibrahim, ya ce asalin filin mallakar gwamnati ne, amma an biya kudin ne saboda dattakun gwamnan.

Ibrahim ya kara da cewa an yi hakan ne don amfanin jama'a, yana mai cewa hakan ya ta'allaka ne ga ci gaban jahar.

"Zuwa yanzu mun biya N873, 214,193,43; wannan shi ne jimillar diyyar da muka biya kan filaye daban-daban da muka samo don ayyukan ci gaba. Dukkanin diyyar an biya kuma ba a bin gwamnati bashi.

“An biya diyya don gine-gine a cikin jahar. Gwamna cikin girmamawa ya ce tunda filin mallakar gwamnati ne, bari mu biya su wani abu. Kasancewar aikin na ci gaba ne," In ji shi.

KU KARANTA: Muhimmancin Tashar Jiragen Ruwa Ga GDP - Hadiza Bala Usman

A wani labarin, Allah ya yi wa tsohon sanatan Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC a jihar Gombe, Sa'idu Kumo rasuwa.

Kumo ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 71 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita, dan shi Abubakar ya sanar wa Premium Times.

Ya rasu a ranar Lahadi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja inda ya sha jinya a kan cutar da ba a bayyana ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.