Na yanke kauna da gwamnatin Buhari, In ji kakakin kungiyar Arewa
- Wani mamba a kungiyar dattawan Arewa ta ACF ya yanke kauna kan shirin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro a Najeriya
- Kakakin kungiyar, Emmanuel Waye, ya ce ya yanke kauna da gwamnatin Shugaban kasa Buhari wajen kawo karshen matsalar da ya addabi kasar
- Waye ya bayyana cewa ba zai iya tafiya zuwa jiharsa ba, Taraba, saboda tsoro, inda ya kara da cewa hakan yake a tsakanin yan arewa da dama
Sakataren kungiyar arewa ta kasa, Emmanuel Waye, ya bayyana cewa ya yanke kauna da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake hira a shirin Channels TV na Politics Today a ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, Waye ya yi korafi a kan tabarbarewar rashin tsaro a kasar.
“Ta yaya zan yi imani da mutumin da ke jagorantar irin wannan abun? Na yi imani da shi a lokacin da na bi shi a matsayin mai rahoto sannan ya fatattaki wasu bakin haure da suka zo kashe mu,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi (dalla-dalla)
“Lokacin da yake son zama Shugaban kasa, na yi imani da shi. Na shaidi yadda mutumin nan ya fatattaki makiya daga kasarmu a 1983 cike da nasara. Amma a yanzu, an yi garkuwa da mutane 300 a jiharsa.”
Yayinda yake bayyana cewa babu tsaro a arewa gaba daya, Waye ya ce babu dan arewa da ke farin ciki da yawan kashe-kashe da hare-hare da ake kaiwa yankin.
Ta bangaren kakakin na kungiyar Arewa, tsoro ya cika shi a yanzu da yake ganin babu tsaro a hanyar zuwa mahaifarsa a jihar Taraba sakamakon rahoton da ake yawan samu na kashe-kashe da hare-hare.
“Ba zan iya zuwa mahaifata ba a Taraba. Wajen gaba daya yana cikin hargitsi, suna kashe mutane a kullun. Ba a bayyana wannan saboda babu mai a Taraba.
“A arewa gaba daya, akwai rashin tsaro. Ban taba jin ban tsira ba kamar yadda nake ji a yanzu. Me zan ce? Kun ga abunda ke faruwa da mutanenmu,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020
Rashin tsaro ya kasance batu da ke tafarfasa a kasar biyo bayan hare-hare da kashe-kashe daga fashi da makami, ta’addanci da sauran abubuwa da ke barazana ga tsaro.
A wani labarin, jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan.
Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.
Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng