Muhimmancin Tashar Jiragen Ruwa Ga GDP - Hadiza Bala Usman
- Alkaluma na mizanin tattalin arziki (GDP) zai bunkasa idan aka zuba dimbin jari a tashoshin jiragen ruwa
- Najeriya ta siya sabbin jiragen ruwa
- Rotimi Amaechi ya bayyana muhimmancin tashoshin jiragen ruwa
Zuba dimbin jari a harkokin tashoshin jiragen ruwa zai kara bayar da gudummawa a alƙaluma na mizanin auna tattalin arziƙi (GDP) na kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Hadiza Bala-Usman ce ta yi wannan ikirarin yayin da ta nanata bukatar karin masu kwazo a bangaren.
Shugabar ta NPA ta lura da cewa, tashoshin jiragen ruwa da gwamnati ke ginawa da kaddarorin da ta samu karkashin jagorancin ta sune mahimman abubuwa wurin inganta tashar a yayin da Najeriya ke kokarin inganta gudummawar bangaren ruwa zuwa ga GDP.
"Don cimma burinmu, muna bukatar samun jiragen ruwa wadanda ke da karfin aiki dan daukan manyan kwantena su zo su yi aiki mai kyau a tashar mu," in ji ta.
Ta kara da cewa don aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata a duk wuraren tashar jiragen ruwa, hukumar ta himmatu don ci gaba da inganta kayan aiki da kayan aikin da za su bunkasa aiki.
“Wannan sadaukarwa ne don tabbatar da cewa dukkan tashoshin ruwa guda shida masu aiki an shirya su don kyakkyawan aiki a kowane lokaci, tace.
Ta kara da cewa "Wannan kudurin ya sanya aka sayi wadannan sabbin jiragen ruwan, MT Musawa & MT Ikoro-Ekiti suka hada kai da sauran jiragenmu guda hudu wadanda suka hada da: MT Daura, MT Ubima, MT Uromi da MT Majiya, wadanda aka kaddamar a shekara ta 2017,"
KU KARANTA: Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari
KU KARANTA: Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
A cikin jawabinsa, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa idan wani ya yi shakku game da mahimmancin sashin teku ga Najeriya da kuma tattalin arzikin duniya ne, abin da ya faru a watanni uku da suka gabata inda tashoshin jiragen ruwa a duk duniya suka kasance a buɗe duk da yawan kulle-kullen da sauran bangarorin ke yi ya kamata ya zama dalilin da ya sa ya kamata a ba da fifiko ga bangaren.
“Ganin kudurin gwamnati na bunkasa wasu bangarorin tattalin arzikin kasa da rage dogaro kan bangaren mai da iskar gas, mun gano muhimmiyar rawar da bangaren ruwa ke takawa wajen tabbatar da mahimman manufofin Maido da Tattalin Arziki da Tsarin Bunkasa (ERGP) ) na wannan gwamnatin." Yace
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng