Allah ya yi wa tsohon sanata kuma jigon APC a arewa rasuwa

Allah ya yi wa tsohon sanata kuma jigon APC a arewa rasuwa

- Cike da alhini tare da tashin hankali yau Lahadi aka tashi da labarin rasuwar Sa'idu Kumo

- Tsohon sanatan kuma mai sarautar garkuwan Gombe ya rasu a asibitin Gwagwalada a Abuja

- Ya taba wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 zuwa 2003

Allah ya yi wa tsohon sanatan Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC a jihar Gombe, Sa'idu Kumo rasuwa.

Kumo ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 71 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita, dan shi Abubakar ya sanar da Premium Times.

Ya rasu a ranar Lahadi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja inda ya sha jinya a kan cutar da ba a bayyana ba.

Allah ya yi wa tsohon sanata kuma jigon APC a arewa rasuwa
Allah ya yi wa tsohon sanata kuma jigon APC a arewa rasuwa. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade

Kumo ya wakilci jihar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003 a karkashin jam'iyyar APP wacce daga baya ta koma ANPP

Ya yi mai bada shawara na musamman ga marigayi tsohon shugaban kasan Najeriya, Umaru Musa Yar'Adua a 2008.

KU KARANTA: Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng